Labari mai dadi: Mata a jihar Bauchi sun samar da hanyar gargajiya ta sarrafawa da adana Tumatir

Labari mai dadi: Mata a jihar Bauchi sun samar da hanyar gargajiya ta sarrafawa da adana Tumatir

Kamar yadda kuka sani Tumatir na daya daga cikin kayayyakin abinci da ake ta’ammali da shi a harkokin yau da kullun wajen sarrafa abinci. Sannan kuma ya kasance abu ne da babu wuya ya lalace.

Wannan dalili ne ya sanya wasu mata a jihar Bauchi suka samar da hanyoyin sarrafawa tare da adana shi a gargajiyance domin sayarwa da kuma amfanin gida.

Wannan hanya da ake bi domin sarrafa shi baida wuya sannan kuma dandanon ba zai sauya ba har tsawon watanni uku koma sama da hakan.

Hanyar sarrafawa na farko shine bayan an tanadi danyen Tumatiri da dama sai a nika shi sannan a tafasa har rowan ya kafe.

Labari mai dadi: Mata a jihar Bauchi sun samar da hanyar gargajiya ta sarrafawa da adana Tumatir
Labari mai dadi: Mata a jihar Bauchi sun samar da hanyar gargajiya ta sarrafawa da adana Tumatir

Zaa bar Tumatiri din ya bushe gaba daya daga nan sai a zuba shi a cikin kwalabe sai a zuba Gishiri dan kadan da kuma mai kadan sai a rufe shi don kada kwayoyin cuta su shiga.

KU KARANTA KUMA: Tazarce: Ya kamata ka barwa matasa mulkin Najeriya – Kungiyar matasan Arewa ga Buhari

Wadannan kwalaben suna dauke da Tumatirin sai a sake tafasa shi zuwa mintuna goma daga bisani sai a cire a ajiye shi a wuri mai kyau don sayar dashi a nan gaba da kuma samun riba har da rage abinda ake kashewa a gida a lokacin da ake karancin Tumatirin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel