Matar Janar Rabe Ta Ki Tafiya Ta Bar Shi a Daji duk da 'Yan Bindiga Sun Ce Ta Tafi

Matar Janar Rabe Ta Ki Tafiya Ta Bar Shi a Daji duk da 'Yan Bindiga Sun Ce Ta Tafi

  • Rahoto ya nuna cewa matar marigayi Janar Rabe Abubakar ta ƙi barin mijinta a hannun masu garkuwa da mutane duk da an ba ta zabin tafiya
  • 'Yarsa ta yabawa mahaifiyarta bisa jarumtar da ta nuna, tare da yin addu'ar Allah ya yi maganin dukkan masu garkuwa da mutane a Najeriya
  • A makon da ya wuce dakarun Operation Fansan Yamma suka ceto matar Janar Rabe Abubakar bayan musayar wuta da 'yan bindiga a Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Ana cigaba da samun bayanai game da abubuwan da suka faru a daji bayan sace tsohon sojin Najeriya, Janar Rabe Abubakar da matar shi.

Janar Rabe Abubakar (Mai ritaya) ya rasu a hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da shi kafin hukumomi su kai ga ceto shi a cikin daji.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Janar Rabe Abubakar da matar shi
Janar Rabe Abubakar a hagu da matar shi da aka ceto a dama. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Me ya faru da matar Janar Rabe?

A wani sako da ta wallafa a X, 'yar marigayi Janar Rabe Abubakar ta bayyana cewa 'yan ta'addan sun ba mahaifiyarsu damar tafiya a cikin daji amma ta ki.

'Yar marigayin ta ce:

"A lokacin da mama da baba suke hannun masu garkuwa da mutane, kusan mako guda bayan sace su, masu garkuwar sun saki mama tare da umartar ta da ta tafi.
"Amma mama ta ce ba za ta tafi ko'ina ba tare da baba ba. Ta gaya masu cewa ko dai su sake su duka biyu tare, ko kuma su kashe su duka biyu."

Ta kara da cewa:

"Mama na daga cikin mata masu ƙarfin hali da na sani. Kaɗan ne daga cikin mata a wannan zamani da za su iya nuna irin wannan jarumta. Allah ya jikansa baba."

Ta kuma yi addu'a tana cewa:

"Ya Allah Ka wulaƙanta masu garkuwa da mutane, da masu ɗaukar nauyinsu, da waɗanda suka haddasa zuwan wannan musiba. Allah Ka saukar musu da musibu, bala'o'i da cututtukan da ba su da magani.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige 'yan bindiga tare da kama wasu a Kaduna

"Allah Ka hana su tuba. Allah Ka sa su yi mutuwa mafi muni."
Marigayi Janar Rabe Abubakar
Tsohon jami'in sojan Najeriya, Janar Rabe Abubakar da ya rasu a hannun 'yan bindiga. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Abin da mutane suka ce

Mutane sun yi martani game da kalaman da 'yar marigayin ta yi, inda galibi suka kasance addu'o'i ne da fatan alheri a gare su.

Zaraha ta ce:

"Allah ya ƙara wa mama lafiya."

Great Khaleed ya ce:

"Na yi aiki tare da Hajiya. Wallahi mace ce mai matuƙar jarumta. Allah Ya ba ta haƙurin rashin baba."

Amifaza Mujeili ta ce:

"Allah ya jikansa da rahama. Allah ya ba ta lafiya."

A ranar 15 ga Yunin 2026 mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook cewa sojoji sun ceto matar.

Onanuga ya magantu kan tsaro

A wani labarin, mun kawo muku cewa mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa ana ruruta matsalar tsaro.

Ya bayyyana haka ne yayin da ya ke amsa tambayoyi game da yadda jama'a ke korafi kan sace-sace da 'yan bindiga ke yi a Najeriya.

Onanuga ya ce akwai matsalar tsaro a wasu yankunan Najeriya amma ba ta riga ta zama ruwan dare ba kamar yadda wasu mutane ke fada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng