Hukumar aikin hajji ta NAHCON ta bukaci maniyyata dasu cigaba da biyan kudin tafiya
- Hukumar aikin hajji ta NAHCON ta jihar Kaduna ta bukaci masu niyya dasu cigaba da biyan kudin tafiya aikin hajjin
- Jami’in kula da harkokin jama’a na hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa an shawarci mutane dasu cigaba da biyan kudin sakamakon Karin lokacin biyan kudin da hukumar tayi
- Abdullahi yace za’a cigaba da biyan kudin ne har zuwa ranar 25 ga watan Afirilu 2018, don hukumar ta samu kai sunayen wadanda suka biya kudin zuwa Helikwatarsu
Hukumar aikin hajji ta NAHCON, ta jihar Kaduna, ta bukaci masu niyya dasu cigaba da biyan kudin tafiya aikin hajjin bana.
Jami’in kula da harkokin jama’a na hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa an shawarci mutane dasu cigaba da biyan kudin sakamakon Karin lokacin biyan kudin hukumar tayi.
Abdullahi yace za’a cigaba da biyan kudin ne har zuwa ranar 25 ga watan Afirilu 2018, don hukumar ta samu kai sunayen wadanda suka biya kudin zuwa Helikwatarsu zuwa 30 Afirilu, 2018.
Ya kara da cewa “shugaban kungiyar, Imam Hussaini Sulaiman Tsoho Ikara ya bayyana cewa tini kungiyar ta samawa mahajjata dakunan kwana a garin Makka”.
KU KARANTA KUMA: Zogala: Maganin dake kashe cutar daji ya kuma hana cutar siga
A kalla mutane 2,200 ne sukayi rajistar tafiya aikin hajjin bana, a cikin 6,636, da hukumar ta NAHCON ta bawa jihar na mahajjatan bana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng