Shugaban ma’aikata na jihar Kogi na farautar rayuwana – Dan jarida ga IGP

Shugaban ma’aikata na jihar Kogi na farautar rayuwana – Dan jarida ga IGP

- Wale Odunsi mataimakin mai tantance labarai, yayi kira ga shugaban hukumar ‘Yan Sanda na kasa akan cewa shugaban ma’aikata na jihar Kogi na farautar rayuwarsa

- A korafin daya kai a helikwatar ‘Yan Sanda yace Edward Onoja ya kirashi ya masa barazanr kisa akan wani labari da ya watsa

- Shugaban ma’aikatan yace labarin karya ne kuma yana bukatar a cireshi daga kafar yada labarai

Wale Odunsi mataimakin mai tantance labarai, yayi kira ga shugaban hukumar ‘Yan Sanda na kasa akan cewa Edward Onoja, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, na farautar rayuwarsa.

A korafin daya kai a helikwatar ‘Yan Sanda yace Edward Onoja ya kirashi ya masa barazanr kisa akan wani labari da ya watsa.

Yace, Shugaban ma’aikatan gwamnan, yace labarin karya ne kuma yana bukatar a cireshi daga kafar yada labarai.

Shugaban ma’aikata na jihar Kogi na farautar rayuwana – Dan jarida ga IGP
Shugaban ma’aikata na jihar Kogi na farautar rayuwana – Dan jarida ga IGP

Odunsi yace ya shawarci Onoja da ya rubuta korafinsa zuwa ga shuwagabannin kungiyar, amma ya kiya.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a kara zabarsa a shekarar 2019 - APC

Yace: “Onoja ya kirashi da misalin karfe 10:39 na safe a ranar Lahadi, 8 ga watan Afirilu, 2018, ta hanyar lambar waya kamar haka 07088698212. Kuma kiran bai wuce na minti uku ba”, a korafin da ya rubuta.

Kokarin samun labari daga bakin Onoja yayi wuya, sakamakon wayarsa bata shiga, kuma an masa sako ta wayar salula amma ba amsa daga gareshi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng