Ben Bruce ya caccaki Garba Shehu kan furuci da yayi
- Ben Bruce ya caccaki kakakin shugaban kasa, Garba Shehu
- Hakan ya biyo bayan kiran yan Najeriya da yayi da malalata da yayi
- Ben Bruce yace babu ayyuka a kasar
Ben Murray-Bruce, Sanata mai wakiltan Bayelsa ta yamma ya caccaki kakakin shugaban kasa, Garba Shehu kan kiran yan Najeriya da yayi da malalata.
Garba Shehu yace yan Najeriya masu lalaci ne kadai ke korafin yunwa.
Da yake maida martini, Ben Bruce yace yan Najeriya ba malalata bane amma basu da aiki saboda rashin aikin yi a kasar.
KU KARANTA KUMA: Noma ya hanani kashe kaina saboda rashin aikin yi – Inji wata matashiya
“Me ke damun kakakin shugabab kasar? Da farko sun kira yan Najeriya da dabbobi. Shin sun san da cewakimanin yan Najeriya miliyan 9 ne ska rasa ayyukansu a shekaru uku da suka shige? Ba wai yan Najeriya basu son yin aiki bane. Suna so suyi aiki, amma ina ayyukan suke?”.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng