Wani dan majalisar Kano yace babu ya Tinubu wajen hadin kan Najeriya

Wani dan majalisar Kano yace babu ya Tinubu wajen hadin kan Najeriya

- Dan majalissar jihar Kano Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu alamace ta hadin kan Najeriya kuma jigo a siyasa

- Dan’agundi yace Tinubu ya gina wata babbar gada a tsakanin bangarorin Najeriya

- Yace gudunmuwar da Tinubu ya bayar a cigaban siyasar Najeriya zai kasance a cikin tarihin Najeriya na har abada

Dan majalissar jihar Kano Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu alamace ta hadin kan Najeriya kuma jigo a siyasa. Dan’agundi yace Tinubu ya gina wata babbar gada a tsakanin bangarorin Najeriya.

Dan’agundi yace gudunmuwar da Tinubu ya bayar a cigaban siyasar Najeriya zai kasance a cikin litattafan tarihin Najeriya na har abada, a matsayin mutumin da ya tsayawa abunda mafi yawan talakawan Najeriya ke ra’ayi.

Dan’agundi ya bayyana haka ne a wurin taron cin abinci da aka gudanarwa mambobin masu wakiltar kananan hukumomi 44 na jihar Kano, don nuna girmamawa ga Bola Ahmed Tinubu.

Wani dan majalisar Kano yace babu ya Tinubu wajen hadin kan Najeriya
Wani dan majalisar Kano yace babu ya Tinubu wajen hadin kan Najeriya

"Munyi shawarar gudanar da wannan biki a jihar Kano, don bayar da dama ga mambobinmu wadanda basu samu damar halartar taron da aka gudanar a jihar Legas ba na cikar Tinubu shekaru 66.

KU KARANTA KUMA: Tabbatar da tsayawar Buhari takara a zaben 2019 zai rufe bakin abokan adawa - Okorocha

"Bayan haka munyi shawarar mayar dashi bikin shekarar shekara, kuma munaso duniya ta san cewa ‘yan Najeriya suna girmama mutane wadanda ta amince dasu”, inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng