Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka

Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka

A kullun garkuwar jikin dan adam cikin bautuwa take domin ganin ta hallaka kwayoyin cututtukan da ke yiwa jikin dan adam kawanya.

Domin haka muka yi amfani da wannan dama domin wayar da kan mutane kan wasu daga cikin nau’ikan abinci da ya kamata su dunga ci domin hana kamuwa da cuta.

Ga wasu daga cikin kalolin abinci 5 da zaa iya ci:

1. Kurkur

Kurkur na dauke da sunadaren da ke kashe kwayoyin cutar bacteria, ana jika shi da ruwa a sha a kullun.

2. Zuma

Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka
Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka

Ana shan zuma babban cokali daya da ruwan dumi da sanyin safiya kafin Karin kumallo.

3. Citta

Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka
Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka

Tana dauke da sinadaren da ke kashe kwayoyin cuta musamman wadanda ke haifar da mura, tari da sauran matsalolin makogwaro.

KU KARANTA KUMA: Yakin neman kujerar shugabancin APC ya karu sakamakon tsoffin gwamnoni da wasu da suka nuna kwadayinsu a kai

4. Tafarnuwa

Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka
Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka

Takarnuwa na kunshe da wani sinadari mai suna Alicin da ke fita da zaran an tauna ko an daka ta. Wannan sinadari ya na bada kariya ga jiki.

5. Abarba

Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka
Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka

Abarba na kashe kwayoyin cututtuka musamman wadanda suke kama baki, hanci, da makogwaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel