Turkashi: Kungiyar Kato da Gora sun hana SARS kama Sanata Dino Melaye

Turkashi: Kungiyar Kato da Gora sun hana SARS kama Sanata Dino Melaye

- A jiya ne akayi badakala a wurin addu’ar fidau na mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Buba Jibril, inda kungiyar kato da gora suka hana hukumar SARS su kama Sanata Melaye

- Hukumar ‘Yan Sanda a kwanakin da suka wuce ne suka sanyashi a cikin wadanda suke nema sakamakon hannu da yake dashi a cikin bawa ‘yan ta’adda makamai

- Jami’an ‘Yan Sandan na SARS sunje makarantar Primary Kabawa wurin addu’ar Fidau ta marigayin inda kungiyar kato da gora suka zagaye sanatan suka hana ‘Yan Sandan kamashi

A jiya ne akayi badakala a wurin addu’ar Fidau ta 8 ga mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Buba Jibril, a Lokoja, jihar Kogi, inda kungiyar kato da gora suka hana hukumar SARS su kama Sanata Melaye mai wakiltar kogi ta Yamma.

Hukumar ‘Yan Sanda a kwanakin da suka wuce ne suka sanyashi a cikin wadanda suke nema sakamakon hannu da yake dashi a cikin bawa ‘yan ta’adda makamai.

Jami’an ‘Yan Sandan na SARS sunje makarantar Firamare Kabawa wurin addu’ar Fidau ta marigayin inda kungiyar kato da gora suka zagaye Sanatan suka hana ‘Yan Sandan kamashi.

Turkashi: Kungiyar Kato da Gora sun hana SARS kama Sanata Dino Melaye
Turkashi: Kungiyar Kato da Gora sun hana SARS kama Sanata Dino Melaye

Bayan addu’ar kungiyar ‘yan kato da gorar dake zagaye dashi suka rakashi zuwa motar shugaban Majalissar Dattijai, Dr Bukola Saraki.

KU KARANTA KUMA: Kano ce kadai Jihar Arewa da ke cikin manyan masu kudin shiga a bara

Bayan nan jami’an sun isa gidan Chief Rasaq Kutepaa GRA, inda ake cin abinci don tarbar Melaye a can su kamashi, sunyi mamakin ganin Melaye a cikin tafiyar shugaban majalissa lokacin da zai tafi filin jirgi na Obajana, inda zasu hau jirgi zuwa Katsina

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng