Mutuwa mai yankar kauna: Saraki yayi alhinin rashin Mustapha Bukar

Mutuwa mai yankar kauna: Saraki yayi alhinin rashin Mustapha Bukar

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya nuna alhini kan mutuwar Sanata mai wakiltan Katsina ta Arewa, Sanata Mustapha Bukar a ranar Laraba, bayan yayi yar gajeriyar rashin lafiya a Abuja.

A wata sanrwa daga mai bashi shawara na musamman a kafofin watsa labarai, Yusuph Olaniyonu a Abuja, Saraki ya bayyana mutuwar Sanata Bukai a matsayin tarin bakin ciki day a zo yan makonni bayan sun rasa Sanata Ali Wakili.

Ya bayyana cewa a lokacin da suka ziyarci marigayin a asibitin bayan sallar Juma’a a makon da ya gabata, sun kyautata zaton cewa zai samu lafiya harma ya dawo kan kujerarsa.

Mutuwa mai yankar kauna: Saraki yayi alhinin rashin Mustapha Bukar
Mutuwa mai yankar kauna: Saraki yayi alhinin rashin Mustapha Bukar

Ya kuma bayyana Bukar a matsayin mutun mai sanyin hali a dukka harkokinsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kuma dai, wani sanatan Najeriya ya sake mutuwa

Daga karshe yayi addu’an Allah ya ji kansa tare da mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin jihar Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng