Abun tausayi: Wata yar gudun hijira ta bayyana halin da suka shiga tare da iyalinta bayan barinsu gida

Abun tausayi: Wata yar gudun hijira ta bayyana halin da suka shiga tare da iyalinta bayan barinsu gida

Kamar yadda kuka sani yankin arewa maso gabashin Najeriya na cikin wani hali na ibtila’i. Daya daga cikin jihar dake fama da wannan hali kuwa it ace jihar Borno.

Sakamakon rikicin Boko Haram al’umman jihar da dama sun zamo marasa galihu inda suka bar mahaifarsu domin tsirar da rayuwasu.

Hakan ce ta kasance ga wata baiwar Allah da ba’a bayyana sunanta ba. Ta bayyana irin gararin da suka shiga tare da mijinta da yaransu bayan barinsu mahaifarsu a jihar Borno.

A cewarta shekarun su biyar kenan da shiga dun iyar gararanba, inda suka rasa gatarsu bayan matar da ta taimake su ta amsa kiran mahallicinta.

Abun tausayi: Wata yar gudun hijira ta bayyana halin da suka shiga tare da iyalinta bayan barinsu gida
Abun tausayi: Wata yar gudun hijira ta bayyana halin da suka shiga tare da iyalinta bayan barinsu gida

Ga laranin da ta bayar a takaace: “Ni, minijina da yaranmu mun bar Borno shekaru 5 da suka shige. Tafiya ce mikakkiya. Mun tsaya a jihar Ogun sannan wata mata ta taimaka mana muka isa Lagas. Tana da kirki sosai sannan ta taimaka matuka a tafiyarmu. Mun zauna tare da mutanen Maiduguri. Kwanakin baya ta mutu.

KU KARANTA KUMA: Abinci kala 5 dake kara karfin garkuwar jiki tare da magance cututtuka

“Amma a nan Lagas, bamu san me ke faruwa ba. Suna kona mana wajen da muka yada zango. Bamu san dalili ba. Basu son Pako a Lagas. An maida mu marasa galihu a gida an kuma maida mu marasa galihu a nan. Ina suke so mu koma”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng