Wani ma’aikacin banki ya bawa wata marainiya ‘yar shekara 13 kwaya sannan ya mata ciki

Wani ma’aikacin banki ya bawa wata marainiya ‘yar shekara 13 kwaya sannan ya mata ciki

- An zargi wani ma’aikacin banki mai shekaru 30 Chidi Agu da bawa wata marainiya ‘yar shekara 13 kwaya ya mata ciki

- Agu ya samu dama ne bayan sirikinsa fasto wanda yarinyarkeyiwa aiki yayi tafiya a cikin shekarar 2017

- Rahoto yazo cewa wata makwabciyarsu ce ta lura da kumburin cikin yarinyar kafin ta sanar da Faston da matarsa

An zargi wani ma’aikacin banki mai shekaru 30 Chidi Agu da bawa wata marainiya ‘yar shekara 13 kwaya ya mata ciki, a SSS kwatas, Jikwoyi, a birnin tarayya.

Agu ya samu dama ne bayan sirikinsa fasto wanda yarinyar ke yiwa aiki yayi tafiya a cikin shekarar 2017. Rahoto yazo cewa wata makwabciyarsu ce ta lura da kumburin cikin yarinyar kafin ta sanar da Faston da matarsa.

Jaridar Punch Metro ta ruwaito cewa, an kai yarinyar Asibiti inda aka tabbatar da cewa yarinyar nada ciki wata biyar.

An fadawa jami’inmu cewa bayan an tambayi yarinyar tace Agu ne yayi mata cikin.

Kawunta John Inyang, yace ya kai kara a ofishin ‘Yan Sanda na Jikwoyi, inda yace ya girgiza lokacin da ya samu labarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kuma dai, wani sanatan Najeriya ya sake mutuwa

Yace yarinyar tana hannunsa tun bayar rasuwar iyayenta.

Ya kara da cewa an kasa shawo kan lamarin a tsakaninsu sakamakon Agu ya kasance kanin matar faston, inda faston da matarsa suka bukaci ya mayar da yarinyar zuwa garinsu a jihar Akwa ibom.

Sun alkawalta cewa zasu ringa tura masa kudi don kula da yarinyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng