NDC: Peter Obi Ya ‘Gano’ Shirin Tinubu na Neman Hana Shi Takara a 2027
- Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya zargi gwamnatin Bola Tinubu yayin da ake shirin zaben shekarar 2027
- Tsohon gwamnan ya kalubalanci masu neman shugabancin kasa, har da Tinubu, da su fito muhawara su bayyana shirinsu ga Najeriya
- Obi ya ce ba son mulki ke tura shi ba, sai dai burin ganin Najeriya ta gyaru, yana mai kira ga matasa su karbi katin zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi zarge-zarge kan gwamnatin Bola Tinubu game da zaben 2027.
Peter Obi ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na kokarin hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027, amma ya ce hakan ba zai hana shi cimma burinsa ba.

Source: Facebook
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da lacca a wani shirin horas da shugabanci da cibiyar 'NextGen Mentorship and Leadership Initiative' ta shirya a Jami’ar Madonna da ke Okija a Anambra, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ndume ya gano matsalar da Tinubu ke fuskanta a fadar shugaban kasa
Obi ya zargi mukarraban Tinubu da yakar shi
A cewarsa, wasu masu karfi a cikin gwamnati sun kuduri aniyar tabbatar da cewa sunansa bai bayyana a takardar zaben shugaban kasa ta 2027 ba.
Ya ce:
“Idan kun san abubuwan da suke yi domin hana ni bayyana a takardar zabe ta 2027, za ku yi mamaki. Amma ba na kallon haka a matsayin cikas, ina kallon inda nake son isa.”

Source: Facebook
Abin da ke karfafawa Obi guiwa
Obi ya kara da cewa abin da ke karfafa masa gwiwa shi ne burin ganin Najeriya ta samu ci gaba da kuma amfanin da al’umma za su samu idan an samu shugabanci nagari.
Tsohon gwamnan Anambra ya kuma kalubalanci duk masu neman shugabancin kasa, ciki har da Bola Tinubu, da su fito muhawara domin bayyana tsare-tsarensu ga ‘yan Najeriya.
Ya ce manufarsa ba wai neman mulki don kansa ba ce, illa ganin Najeriya ta zama kasa mai aiki yadda ya kamata, inda kowa zai samu damar cimma burinsa.
Obi ya bukaci dalibai da matasa su mallaki katin zabe, yana mai cewa kada su zabe shi saboda asalinsa na kabilar Igbo, sai dai idan sun ga ya fi cancanta.
Da yake magana kan matsalar tsaro, ya yi alkawarin yakar laifuffuka da rashin tsaro idan aka ba shi damar jagorantar kasar nan a gaba, cewar Punch.
Har ila yau, Obi ya ce hukuncin kotun tarayya da ya soke wani umarni da ya shafi rajistar jam’iyyar NDC ba zai dakatar da burinsa na siyasa ba.
Ya ce:
“Ba za su iya hana ni ba. Za su gaza, muna da yakinin cewa muradin jama’a ne zai yi nasara a karshe.”
A karshe, ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da zaman lafiya tare da kare dimokuradiyya, yana mai cewa akwai bukatar hadin kai domin ceto kasar daga matsalolin da take fuskanta.
NDC ta magantu bayan hukuncin kotu
Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar NDC ta yi fatali da hukuncin babbar kotun tarayya mai zama a Lakoja, wanda ya rusa rijistar da aka mata a matsayin jam'iyyar siyasa.
NDC ta tabbatar wa Peter Obi, Kwankwaso da sauran 'yan takararta cewa hukuncin ba zai hana jam'iyyar shiga babban zaben 2027 ba.
A sanarwar da ta fitar yau Juma'a, jam’iyyar NDC ta ce ta umarci lauyoyinta su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.
Asali: Legit.ng
