Allah ne zai zabi mai gado na ba ‘yan siyasar Abuja ba - Shettima

Allah ne zai zabi mai gado na ba ‘yan siyasar Abuja ba - Shettima

- Gwamna Kashim Shettima ya bayyna cewa ba shi masaniyar wanda zai canje shi

- A cewarsa ya barwa Allah zabi na wanda zai gaje shi

- Amma ya jaddada cewa wanda zai gaje shi din zai kasance ba mai yawan shekaru ba ne

Gwamnan Kashim Shettima na jihar Borno ya bayyana cewa ba shi masaniyar wanda zai maye gurbinsa bayan wa’adin sa ya kare a watan Mayu na 2019 mai zuwa.

Kashim ya ce ya bar wa Allah ya zabar wa al’ummar jihar wanda ya fi dacewa.

Sai dai kuma ya jaddada cewa wanda zai gaje shi din zai kasance ba mai yawan shekaru ba ne, zai kasance daga cikin ‘yan siyasa masu tasowa.

Ya kara da cewa wannann abu ko kadan bai yi wa wasu ‘yan-siyasar-Abuja ‘yan asalin jihar dadi ba.

Allah ne zai zabi mai gado na ba ‘yan siyasar Abuja ba - Shettima
Allah ne zai zabi mai gado na ba ‘yan siyasar Abuja ba - Shettima

Shettima ya yi wadannan jawabi ne a lokacin da karbi bakuncin kwamishinonin sa da suka je gidan gwamnati domin wani taro na cin abincin rana.

Sai dai kuwa wadannan kalamai sun nuna cewa ana wani irin zama da za a ce ta-ciki-na-ciki ne kawai a tsakanin mambobin APC na jihar Barno.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta ya bayyana cewa sauya shekar wasu gwamnoni kuma mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayi masu ciwo sosai.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Miyetti Allah akan barazanar tsige Saraki daga kujerarsa

Ya bayyana hakan a Daura, jihar Katsina lokacin da ya jagoranci sauran gwamnonin APC wajen ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bikin babban Sallah tare da shi.

Yayi bayanin cewa ciwon da abun yayi masu ya kasance saboda sunyi tarayya da juna a matsayin yan uwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel