"Ba Su Cancanci Rayuwa ba", Gwamna Uba Sani Ya Fadi Hukuncin da Ya Dace da 'Yan Bindiga

"Ba Su Cancanci Rayuwa ba", Gwamna Uba Sani Ya Fadi Hukuncin da Ya Dace da 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa bai gamsu da batun sake bayar da dama ta hanyar gyara halin 'yan ta'adda ba
  • Sanata Uba Sani ya bayyana cewa 'yan bindiga 'yan ta'adda ne domin suna kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata hukumomin tsaro su dauki tsauraran matakai a kan duk masu kashe mutane da yin garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan hukuncin da ya dace da 'yan bindiga da 'yan ta'adda.

Uba Sani ya bayyana cewa 'yan bindiga da 'yan ta'adda ba su cancanci sake samun dama ba, inda ya nace kan cewa ba su da haƙƙin ci gaba da rayuwa.

Uba Sani ya yi magana kan 'yan bindiga
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels tv, ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

'Yaran jagoran 'yan bindigan da suka sace Janar sun sake sabon ta'addanci a Katsina

Me Uba Sani ya ce kan 'yan ta'adda?

Uba Sani, wanda ya ce dole ne a shafe 'yan ta'adda baki ɗaya, ya jaddada cewa ayyukan 'yan ta'addan sun hana mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba cin moriyar rayuwarsu.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa 'yan bindiga da 'yan ta'adda ba su cancanci damar gyaran hali da sake haɗa su cikin al'umma ba.

Yace kashe mutane da kuma yin garkuwa da mata da yara suna cikin dalilan da suka sa dole ne hukumomin tsaro su ɗauki kwararan matakai a kan waɗannan ƙungiyoyi.

"Ban yarda cewa sun cancanci samun dama ta biyu ba saboda, a nawa ra'ayin, su 'yan ta'adda ne. 'Yan bindiga 'yan ta'adda ne."

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya ce a kawar da 'yan ta'adda

Ya ƙara da cewa duk wanda ya kashe rayuka da gangan kuma ya lalata garuruwa ba za a iya ɗaukar shi a matsayin wanda ya cancanci samun sassauci ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da 'yan bindiga suka kashe babban limami har da sace matan aure a Sokoto

“Idan ka kira su 'yan ta'adda, hakan yana nufin mutane ne da suka kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Tabbas, ba su da haƙƙin rayuwa; dole ne a kawar da su."

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya ce ya kamata a kashe 'yan bindiga
Gwamna Uba Sani na Kaduna na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Twitter

Gwamnan ya nace kan cewa dole ne gwamnatoci su ba da fifiko ga gudanar da kariya ga 'yan ƙasa masu bin doka, yana mai jaddada cewa waɗanda ke da hannu a hare-haren ta'addanci ya kamata su fuskanci fushin jami'an tsaro.

"Ɗan ta'adda ɗan ta'adda ne. Yana iya kisan kai, yana iya yin barna, saboda haka, kamata ya yi a kashe shi."

- Gwamna Uba Sani

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

​Mummunan harin da 'yan bindigan suka kai a garin Sayaya, ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane bakwai, har da mace guda daya.

Mazauna yankin sun alaƙanta sabon harin da 'yan bindigan suka kai da janyewar dakarun sojoji na rundunar ‘Operation Fansan Yamma’.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng