Yan sanda sun cafke wani dan shekara 19 da ya sace $4000 yana bushahar sa a Gombe

Yan sanda sun cafke wani dan shekara 19 da ya sace $4000 yana bushahar sa a Gombe

- Yan sandan Gombe sun kama wani matashi dan shekara 19

- An kama matashin ne dauke da dala 4000 inda yake balla bushashar sa da kudin

- Matashin yace ya sato kudaden ne daga wani ubangidansa da yake yiwa aiki

Rundunar yan sanda a jihar Gombe sun samo dala 4,000 (kimanin naira miliyan 1.3) daga hannun wani matashin yaro dan shekara 19 bayan sun kama shi a garin Pindiga dake karamar hukumar Akko dake jihar.

Kakakin rundunar Mary Malum ta tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Gombe inda ta kara da cewa sun kama Idris Abubakar da wadannan dalolin ne, da kuma Naira 21,000, turamen atanfofi biyu, takalma biyu, nauran sauraron sauti,wayar tarho da alewar chakulat bakwai.

Yan sanda sun cafke wani dan shekara 19 da ya sace $4000 yana bushahar sa a Gombe
Yan sanda sun cafke wani dan shekara 19 da ya sace $4000 yana bushahar sa a Gombe
Asali: Depositphotos

Ta ce rundunar ta kama Abubakar ne bayan wani ya kawo musu karan yadda yake ta bushashar sa da kudaden ranar 19 ga watan Agusta a ofishin su.

KU KARANTA KUMA: 2019: Matasan Arewa sun tsayar da Saraki a matsayin shugaban kasa

“Daga nan ne muka fara bibiyar sa a hankali har muka kama shi. Abubakar ya tabbatar mana cewa ya sato kudaden ne a gidan wani dan kasar Lebanon da yake yi wa aiki a garin Kano.

A karshe malum ta ce sun aika wa shashen da ake hukunta masu aikata irin wannan laifi domin ci gaba da bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel