Wata Sabuwa: PRP Ta Kawo Cikas a Shirin Kirkiro Rundunar 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

Wata Sabuwa: PRP Ta Kawo Cikas a Shirin Kirkiro Rundunar 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

  • Jam’iyyar adawa ta PRP ta yi watsi da kudirin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa rundunar sandan jihohi a Najeriya
  • Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun amince da kudirin yayin da Shugaba Bola Tinubu da gwamnoni suka nuna goyon baya ga tsarin
  • PRP ta ce gwamnatin Tinubu ba ta da amincewar jama’a da za ta jagoranci irin wannan babban sauyi a harkar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar PRP ta bayyana rashin amincewarta da shirin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya da ke neman kafa tsarin ‘yan sandan jihohi a fadin kasar nan.

Hakan na zuwa ne bayan Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun amince da kudirin kafa rundunar yan sandan jihohi da nufin magance matsalar tsaro.

Hakeem.
Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: UGC

Jaridar The Cable ta ce kudirin ya nemi gyaran kundin tsarin mulkin na neman cire harkokin ‘yan sanda daga jerin ayyukan gwamnatin tarayya kadai zuwa tsarin da jihohi za su iya kafa nasu rundunonin ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu kan batun kafa yan sandan jihohi a Najeriya

Kudirin ya samu goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnoni, musamman yayin da matsalolin tsaro ke ci gaba da addabar sassa daban-daban na Najeriya.

PRP ta nuna damuwa kan shirin 'yan sandan jihohi

A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, PRP ta ce tana matukar damuwa da yunkurin kafa ‘yan sandan jihohi a wannan lokaci.

Jam’iyyar ta ce gwamnatin Tinubu na kokarin aiwatar da wannan sauyi ne a lokacin da amincewar jama’a da kuma yadda take tafiyar da mulki ke fuskantar kalubale.

A cewar PRP, Najeriya na bukatar a sake nazarin tsarin tsaro baki daya domin magance matsalar rashin tsaro da kuma dawo da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro.

Dalilin da PRP ba ta goyon bayan yunkurin

Jam’iyyar ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ba ta da isasshen karfi da goyon bayan jama’a domin jagorantar irin wannan babban sauyi a tsarin tsaron kasar.

Ta ce gwamnatin ta gaza sarrafa cibiyoyin tsaro yadda ya kamata, don haka yunkurin kafa ‘yan sandan jihohi a wannan lokaci na haifar da tambayoyi da damuwa.

Kara karanta wannan

NASFAT ta ja hankalin musulmai, ta nemi su taimaka kan matsalar tsaron Najeriya

A rahoton tashar Channels tv, PRP ta bayyana cewa:

“Shirin samar da ‘yan sandan jihohi a wannan lokaci abin zargi ne, kuma ya kamata a yi watsi da shi.”
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin wani taro da ya halarta a kasar waje Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Jam’iyyar adawar ta kara da cewa ya kamata a bari a gudanar da zabukan gaba cikin gaskiya da amincewar jama’a kafin a dauki muhimman matakai irin na sauya tsarin aikin ‘yan sanda.

PRP ta bukaci gwamnatin Tinubu ta kara himma wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar al’ummar Najeriya maimakon mayar da hankali kan gyaran kundin tsarin mulki domin kafa ‘yan sandan jihohi.

Majalisa ta amince da kafa yan sanda

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Amincewar majalisar na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika mata bukatar kafa rundunar yan sandan jihohi a Najeriya.

Rahotanni sun nun cewa kudirin ya samu goyon bayan galibin sanatoci, inda suka bayyana muhimmancin kafa rundunar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262