PDP ta bukaci Tambuwal, Atiku, Kwankwaso da sauransu da su amince da duk sakamakon da zaben fidda gwani ta fitar

PDP ta bukaci Tambuwal, Atiku, Kwankwaso da sauransu da su amince da duk sakamakon da zaben fidda gwani ta fitar

A kokarin ganin an gabatar da zaben fidda gwani na gaskiya da amana, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa ya gana da ‘yan takarar kujerar shugaban kasa a Abuja a daren ranar Laraba, 29 ga watan Agusta.

Tawagar ta jam’iyyar PDP sun samu jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus.

Sauran mambobin da suka halarci wannan ganawar sun hada da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na kasa da wasu mambobin kungiyar amintattu na jam’iyyar.

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Plateau, Jona Jang, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi.

PDP ta bukaci Tambuwal, Atiku, Kwankwaso da sauransu da su amince da duk sakamakon da zaben fidda gwani ta fitar
PDP ta bukaci Tambuwal, Atiku, Kwankwaso da sauransu da su amince da duk sakamakon da zaben fidda gwani ta fitar
Asali: Depositphotos

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da tsohon ministan ayyuka na musamman, Alhaji Kabir Tanimu Turaki sun hallara.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Zan lallasa Buhari idan aka bani tikitin takara -Lamido

Wadanda basu samu halartan taron ba sun hada da Ahmed Datti, Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwanbo da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.

Sun yi ganawar ne a cikin sirri.

An tattaro cewa Secondus ya fadama yan takarar cewa jam’iyyar zata gabatar da zaben fidda gwani na gaskiya da amana.

Ya kuma ba su tabbacin cewa kwamitin masu ruwa da tsaki bata da wani dan takara da tafi so a cikinsu, inda ya kara da cewa babban burin jam’iyyar shine ta kore gwaamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2019.

Ya fada masu cewa jam’iyyar da sauran shugabanni a kasar zasu so yan takaran sun hada kansu su marawa du wanda yayi nasa baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel