Dalilin da yasa na zabi cigaba da kasancewa a APC – Shehu Sani
- Sanata Shehu Sani yace ya yanke hukuncin ci gaba da kasancewa a jam'iyyar APC saboda Shugaba Buhari da Oshiomhole sun sanya baki a lamarin
- Ya yi kira ga fusatattun mammbobin APC a majalisar dokokin kasar da su ajiye son zuciya sannan su hada hannu tare da jam’iyyar wajen kawo ci gaba a lamuran al’umman kasar
- Yace duk da cewar shi baya ra’ayin tikiti kai tsaye, amma dai cewa jam’iyyar tayi alkawarin yanta duk masu biyayya
Sanata Shehu Sani (APC-Kaduna ta tsakiya) ya bayyana cewa ba wai don an magance rikicinsa da shugabancin jam’iyyar na jihar Kaduna ba ne yasa shi ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ba, sai dai saboda sanya bakin da Shugaba Buhari da shugaban jam’iyyar na kasa suka yi.
Sani ya bayyana hakan a lokacin ziyarar bikin Sallah da ya kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta, NAN ta ruwaito.
Legit.ng ta tattaro cewa sanatan yayi kira ga fusatattun mammbobin APC a majalisar dokokin kasar da su ajiye son zuciya sannan su hada hannu tare da jam’iyyar wajen kawo ci gaba a lamuran al’umman kasar.

Kan ko an tabbatar masa da samun tikitin sake takara kai tsaye a 2019, Sani yace duk da cewar shi baya ra’ayin tikiti kai tsaye, amma dai cewa jam’iyyar tayi alkawarin yanta duk masu biyayya.
KU KARANTA KUMA: Babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da yayi ma talaka aiki kamar Buhari
Ya bayyana cewa ya zama dole a bi ka’ida wajen kyautatawa mambobin da suka yiwa jam’iyyar biyayya.
Idan zaku tuna a baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Shehu Sani yayi barazanar barin APC kan zargin gaza magance matsalar cikin gia dake faruwa a jam’iyyar cikin shekara uku da shuka gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng