2019: Kungiyar matasa a Gombe na so matashi ya zama gwamnan jihar

2019: Kungiyar matasa a Gombe na so matashi ya zama gwamnan jihar

- Kungiyar matasa a jihar Gombe na so matashi ya zama gwamnan jihar

- Sun shawarci kungiyoyin siyasa da su sanya matasa wajen zaben fidda gwani

- Hakan ya biyo bayan amincewa da dokar ba matasa shiga a dama dasu a siyasa da Shugaba Buhari ya sanya hannu

Wata kungiyar matasan jihar Gombe mai suna Gombe State Youth Progressives Development, tayi kira ga jam’iyyun siyasa a jihar da su sanya matasa a matsayin yan takara a zaben fidda gwani na gwamna da za’a gudanar.

A wata sanarwa da kungiyar ta saki a jiya ta hannun shugabanta, Aliyu Ahmed ya bayyana cewa Allah ya albarkaci jihar da matasa masu kwazo kama daga yan siyasa, da yan kasuwa dake neman tikitin kujerar gwamna a jam’iyyun APC da PDP, manyan jam’iyyun siyasar jihar.

2019: Kungiyar matasa a Gombe na so matashi ya zama gwamnan jihar
2019: Kungiyar matasa a Gombe na so matashi ya zama gwamnan jihar
Asali: UGC

Ahmed yace duba ga sanya hannun da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a dokar ba matasa damar siyasa toh ya kamata APC da PDP suba matasa damar tsayar da matasa a matsayin yan takara.

KU KARANTA KUMA: A yanzu babu wani yanki dake karkashin kulawar Boko Haram a Najeriya - Buhari

Kungiyar tace lokaci yayi da ya kamata a bari matasa su taka rawar ganinsu a siyasa domin kawo cigaba a jihar.

Ahalin da ake ciki, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi bayanin dalilin da yasa ba’a kaddamar da wani kwamiti da zai tantance yan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar ba tukuna.

Baya ga yan takarar kujerar shugaban kasa, jam’iyyar bata ambaci wani kwamiti da zai yi duba ga takardun sauran yan jam’iyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng