Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Miyetti Allah akan barazanar tsige Saraki daga kujerarsa

Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Miyetti Allah akan barazanar tsige Saraki daga kujerarsa

- Kungiyar matasan Arewa ta gargadi kungiyar Miyetti Allah akan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

- Sun shawarce su da taimaka wajen kawo karshen kashe-kashe maimakon sanya baki a siyasa

- Shugaban kungiyar yace basu da hurumi wajen tsige Saraki daga matsayinsa

Kungiyar matasan Arewa kan zaman lafiya da tsaro ta shawarci kungiyar Miyetti Allah da ta mayar da hankali wajen taimakawa domin kawo karshen kashe-kashe maimakon sanya baki a harkokin siyasa.

Shugaban kungiyar na kasa, Salisu Magaji ya bayar da wannan shawara a wata sanarwa da ya gabatar a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta, a Abuja, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Miyetti Allah akan barazanar tsige Saraki daga kujerarsa
Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Miyetti Allah akan barazanar tsige Saraki daga kujerarsa

Magaji ya nuna kulawa akan wani jawabi da aka alakanta da Garus Galolo, shugaban kungiyar na jihar Benue, inda ya bukaci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da yayi murabus daga kujerarsa ko kuma sun tursasa shi yin hakan.

KU KARANTA KUMA: Sauya shekar Gwanonin APC yayi mana ciwo sosai - Okorocha

Ya bayyana cewa sanatoci ne suka zabi Saraki sannan kuma kaso biyu cikin uku na yan majalisa ne kadai zasu iya cire shi daga kan kujerarsa kamar yadda doka ta tanadar.

Magayi yayi mamakin cewa kodai kungiyar ta siyasa ce da har take barazanar tsige Saraki daga mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng