Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

A ranar Litinin, 27 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta fitar da jerin ayyukan ginin tituna da gadoji da ta ce tana yi a kudu maso gabashin Najeriya.

Ministan bayanai da al'addu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa ayyukan sun hada da tituna da gadoji 69 a yankin.

A wata sanarwa daga hannun kakakin ministan, Segun Adeyeni yace ko da yake an bayar da wasu daga cikin kwangilolin gina hanyoyi da gadodjin kafin hawan wannan gwamnati kan mulki, amma ba a ba da kudi da yawa ko ma a wani lokacin ba a bayar da su ba kwata-kwata, domin gudanar da ayyukan.

Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69
Gwamnatin Buhari ta gina wa 'yan kudu tituna da gadoji 69

Lai ya ce ayyukan da ake yi sun shafi dukkan jihohi biyar na yankin kuma suna matakai daban-daban na kammaluwa.

KU KARANTA KUMA: Bolaji Abdullahi ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar gwamnan Kwara

Ya kara da cewa an samu kudin yin ayyukan ne daga kasafin kudin da gwamnati ta yi da kudin da aka samu daga takardun lamuni na Sukuk da kuma asusun shirin shugaban kasa na aiwatar da manya ayyuka.

Daga karshe ya ce gwamnati na duba yiwuwar amfani da kudin da aka kwato daga barayin kudin gwamnbati domin aiwatar da ayyyukan ci gaban kasa a duk fadin Najeriya.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Leah Sharibu, daya daga cikin yan matan Dapchi 119 da yan tada kayar bayan Boko Haram suka sace a makarantan sakandaren gwamnati na mata a garin Dapchi, jihar Yobe, ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya ceceta.

Leah Sharibu ce kadai ba’a saki ba lokacin da aka saki sauran yan matan saboda ta ki sauya addininta zuwa Musulunci.

A wani hoto da odiyo na nuna cewa tana da rau. Jaridar The Cable ta samu rahoto na musamman da ya kunshi hotonta da gajeren jawabi. A jawabin, ta bukaci Buhari ya cetota kuma a taimakawa iyayenta da sauran iyalai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel