2019: Tazarcen Buhari zai ba yan Igbo damar shugabancin kasa – Idiga

2019: Tazarcen Buhari zai ba yan Igbo damar shugabancin kasa – Idiga

Wata kungiyar siyasa mai kokarin ganin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarar zarcewa a zaben 2019 mai suna Good Governance Ambassadors of Nigeria (GOGAN) tayi kira ga mutanen yankin kudu maso gabas da su marawa shugaban kasar baya domin ya samar masu hanya da mutumin Igbo zai zamo shugaban kasa a 2023.

Shugaban kungiyar na kasa, Cif Felix Idiga wanda yayi wannan kira a lokacin ganawar kungiyar a Abuja, ya bukaci yan Igbo da kada su bari wannan dama ya kubuce masu na ganin yankin su sun wadanda zasu gaji Shugaba Buhari.

Cif Idiga yayi gargadin cewa yankin kudu maso gabas na iya rasa wata dama har sai shekaru ashiri masu zuwa idan har basu yi amfani da damarsu da hikima ba.

2019: Tazarcen Buhari zai ba yan Igbo damar shugabancin kasa – Idiga
2019: Tazarcen Buhari zai ba yan Igbo damar shugabancin kasa – Idiga
Asali: Facebook

Yayi gargadin cewa kada su kuskura su tafka kuskure domin basu taba samun zababben shugaba a mulkin damokradiyya ba tun bayan da Najerita ta samu yanci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa tsegumi akan ci gaba da kasancewa kakakin majalisar dattawa Yakubu Dogara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yawaita a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta lokacin da daya daga cikin hadiminasa ya shiga takarar kujerar majalisar dokokin jihar Bauchi.

Iliya Habila, daya daga cikin mataimakansa a kafofin watsa labarai zai tsaya takarar kujerar dan majalisa a mazabar Bagoro karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel