Ku sake zaba na a matsayin shugaban kasa a 2019 – Buhari ya roki mata

Ku sake zaba na a matsayin shugaban kasa a 2019 – Buhari ya roki mata

- Shugaba Muhammadu Buhari yayi godiya ga matan Najeriya kan gudunmawar da suka bashi a zaben 2015

- Ya roke su da su sake zabarsa a zaben 2019 mai zuwa

- Buhari ya yaba da irin rawar ganin da mata ke takawa a siyasar kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi godiya ga matan Najeriya da suka zabe shi a 2015 sannan ya bukace su da su sake maimaita hakan a 2019.

Yayi kiran ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta lokacin wani taro na kungiyar mata masu neman takara wadda kungiyar mata na kasa tare da ofishin uwargidan shugaban kasa suka shirya.

Buhari ya bayyana cewa mata ne keda kuri’u sama a kaso 50 cikin 100 sannan kuma cewa sun fi takwarorinsu maza jajircewa.

Ku sake zaba na a matsayin shugaban kasa a 2019 – Buhari ya roki mata
Ku sake zaba na a matsayin shugaban kasa a 2019 – Buhari ya roki mata
Asali: Facebook

Shugaban kasar wadda yace taron na nuna kaimin matan Najeriya, wadda aka shirya shi domin tallafawa mata masu takarar siyasa a harkar siyasar kasar, inda ya bayyana cewa sun fi dogara da kuri’un mata domin suka jajirce akan maganarsu.

Shugaban kasar yayi amfani da wannan dama wajen bayyana cewa kalubalen da aka fuskanta tun 2015 ya ba da damar sanin hanyoyin inganta ababen more rayuwa, Karin ayyukan yi da kuma karin abinci ga yan Najeriya.

A halin dake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin Shugabna kasa Muhammadu Buhari ta fitar da miliyoyin ýan Najeriya daga kangin talauci a shekaru uku da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: PDP ta bukaci Tambuwal, Atiku, Kwankwaso da sauransu da su amince da duk sakamakon da zaben fidda gwani ta fitar

Yana martani ne akan jawabin da Firai Minista Theresa May da tace kasar Najeriya ce ke da matalauta mafi yawa.

Osinbajo yace a wannan lokaci, gwamnatin ta zuba tushe mai karfi domin inganta tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kuma bayar da dama ga hukumomi masu zaman kansu domin ci gaba ta hanyar shirin farfado da tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel