An Jingina Barazanar Tsaro ga Galibin Masu POS, EFCC za Ta Fara Yaki da Su

An Jingina Barazanar Tsaro ga Galibin Masu POS, EFCC za Ta Fara Yaki da Su

  • Hukumomin EFCC da CAC za su fara yaki da masu gudanar da sana'ar POS da ba su yi da rajista, saboda ganin hakan barazana ne ga tsaro
  • Rahoto ya nuna cewa CAC ta bayyana cewa akalla kimanin 20 cikin 100 ne kawai na masu POS a Najeriya suka yi rajista da ita duk da kiran da ta yi
  • Hukumar EFCC ta ce ta fara bincike kan Mukhtar Muhammad da wasu kamfanonin canjin kudi uku a Najeriya tun kafin Amurka ta sa masu takunkumi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar EFCC da CAC sun kaddamar da wani mataki na hadin gwiwa domin dakile ayyukan masu gudanar da harkar POS da ba su yi rajista ba.

Hukumomin sun yi gargadin cewa irin wadannan ayyuka na iya zama babbar barazana ga tsaron kasa da tsarin hada-hadar kudi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna ya bukaci a haramta almajiranci a Najeriya

Wasu masu aikin POS
Yadda ake hada-hada a wajen wasu masu POS. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

EFCC ta wallafa a Facebook cewa ta riga ta fara bincike kan wani mai sana'ar canjin kudi (BDC) da ke Legas, Mukhtar Muhammad da Amurka ta kakabawa takunkumi.

Korafin hukumar CAC kan masu POS

Shugaban kwamitin gudanarwa na CAC, Ibrahim Adah, ya yi korafi kan masu POS yayin wata ziyara da ya kai wa shugaban EFCC, Ola Olukoyede, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Adah ya ce kashi 20 cikin 100 ne kawai na masu gudanar da harkar POS a kasar nan suka yi rajista a CAC. lamarin da ya ce ya saba wa dokar kamfanoni ta CAMA ta shekarar 2020 da kuma ka'idojin CBN na shekarar 2026.

Ya ce CAC na neman hadin kan EFCC domin tabbatar da cewa masu POS a fadin kasar nan sun bi ka'idojin rajista, tare da samar da ingantaccen kundin bayanansu domin amfani da shi wajen binciken jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da shugaban Fulani na Miyetti Allah bayan cafke shi kan $2.5m

Taron EFCC da CAC a Abuja
Jami'an hukumar EFCC da na CAC bayan taro a Abuja. Hoto: EFCC
Source: Facebook

Martanin hukumar EFCC

Da yake mayar da martani, shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana ayyukan POS da ba a tsara ba a matsayin babbar barazana ga tsarin hada-hadar kudi na Najeriya.

The Guardian ta rahoto ya ce idan ba a tsara ayyuka irin wadannan da ke da muhimmanci ba, hakan zai jawo matsaloli masu yawa ga tsarin hada-hadar kudi na kasar.

Olukoyede ya kuma bayyana cewa EFCC na gudanar da bincike kan kimanin kamfanoni 200 da CAC ta mika mata, inda ya ce binciken ya fara samar da bayanai masu muhimmanci.

Majiyoyi daga EFCC sun ce hukumar ta kammala muhimman sassa na binciken da take yi, tare da shirin gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu, kafin gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba masu takunkumi.

EFCC ta magantu kan Bodejo

A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar EFCC ta fitar da sanarwa game da shugaban kungiyar Miyetti Allah da aka kama a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sakkwato ta yi magana kan rahoton da ake yadawa game da Bello Turji

A bayanin da ta yi a makon nan, EFCC ta ce za a gurfanar da Bello Bodejo a gaban kotu bisa wasu tuhume-tuhume da ake masa da suka shafi kudi.

Manyan tuhume-tuhumen da ake yi wa shugaban Miyetti Allah sun hada da karbar kudi a hannu da suka wuce ka'idar da aka gindaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng