Alhazzan jihar Sokoto rukunin farko sun iso gida Najeriya

Alhazzan jihar Sokoto rukunin farko sun iso gida Najeriya

Bayan kammaluwar aikin hajji, Alhazai sun fara komawa kasashensu na haihuwa. Dama dai da zaran an kammala aikin hajji hankalin ko wani Alhaji da Hajiya kan koma gida, domin ganin sun isa ga yan uwansu bayan wasu makonni wajen ibadah.

Hakan ce ta kasance ga Alhassan kasar Najeriya inda a yanzu haka rukunin farko na rukunin farko na mahajattan jihar Sokoto suka iso gida Najeriya.

Alhazzan da yawan su suka kai 259 sun zauka ne a filin jirgin sauka da tashi na Sarkin Musulmi Abubakar III dake Sokoto.

Alhazzan jihar Sokoto rukunin farko sun iso gida Najeriya (hotuna)
Alhazzan jihar Sokoto rukunin farko sun iso gida Najeriya

Kwamitin da Gwamnatin jihar ta sanya domin tarbon su karkashin jagaorancin tsohon Kwamishinan lamurran addini, Honarabul Mani Maishinko Katami ne ya tarbi Alhazzan.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Buhari na bogi ya damfari masu neman aiki 14 a Niger

Ya kuma yi masu barka da zuwa da isar da sakon kowa ya tabbata anyiwa fasfon din shi tambari kafin ya wuce gida.

A bangare daya mun ji cewa wani jirgin MaX ya riga ya taso daga kasar Saudiyya dauke da Alhazan Kogi 446 duk suna kan hanyar su na dawo wa kasa Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel