Kwankwaso ya sha alwashin kayar da Buhari a zaben 2019

Kwankwaso ya sha alwashin kayar da Buhari a zaben 2019

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano ya kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaben 2019 karkashin inuwar jam'iyyar PDP mai adawa a wani taron gangami da ya gudana a birnin Abuja, in da ya lashi takobin karbe kujerar mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a yanzu, Rabiu Musa ya kaddamar da ra’ayinsa na tsayawa takara a zaben 2019 karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kwankwaso ya bayyana kudirin nasa ne a wajen wani taron gangami da ya gudana a babban birnin Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya sha alwashin kwace mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zab mai zuwa.

Taron Kwankwaso ya gudana ne a ranar Laraba a Otel din Chida de ke Utako a birnin Abuja bayan hana shi amfani da dandalin Eagle Square da akayi.

Kwankwaso ya sha alwashin kayar da Buhari a zaben 2019
Kwankwaso ya sha alwashin kayar da Buhari a zaben 2019
Asali: Depositphotos

Taron ya samu halartar magoya bayan tsohon gwamnan na Kano daga sassa daban daban na Najeriya kuma yawancinsu sun sanya jajayen huluna don nuna goyon bayan ga Kwankwaso da aka san shi da sanya jar hula.

A dogon jawabin da ya gabatar, Kwankwaso ya yi alkawarin tunkarar matsalar tsaro da bunkasa tattalin arziki da inganta kayayyakin more rayuwa da bayar da ilimi matukar aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace duk bita da kullin da za’ayi a yi, amma fa babu gudu babu ja da baya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Jaridar daily trust ce ta ruwaito kaakakin Sanata Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin tana cewa babu wani barazana ko bita da kullin da zai yi tasiri akan Kwankwaso har ta kai ga ya fasa kaddamar da takararsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamitin yakin neman zaben Sanatan tana cewa a ranar Talata ta samu wasika daga manajan kamfanin dake kula da dandalin Eagles Square cewa an hanasu gudanar da taron a wurin, don gudun kada su takura ma ma’aikata duk da sun biya kudinsu tun mako guda daya wuce.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel