"Ba Yan Bindiga ba ne," Rundunar 'Yan Sanda Ta Fadi Wadanda Aka Gani Dauke da Makamai a Bidiyo
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta karyata zargin cewa jami’anta suna mu’amala da ‘yan bindiga a jihar Katsina
- Hakan na zuwa ne bayan wani bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna ‘yan sanda suna gaisawa da wasu dauke da makamai a kan babura
- ‘Yan sanda sun ce mutanen da ke cikin bidiyon ba ‘yan bindiga ba ne, mambobin kungiyar sintiri ta bijilanti (VGN) ne da mafarauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta karyata rahotannin da ke yawo cewa wasu jami’anta suna mu’amala ko hada kai da ‘yan bindiga a jihar Katsina.
Zargin ya samo asali ne daga wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, wanda ya nuna wasu jami’an ‘yan sanda suna gaisawa da wasu dauke da makamai a kan babura.

Source: Twitter
A bidiyon wanda tsohon sanatan Daura, Ahmad Babba Kaita ya wallafa a Facebook, an ga 'yan sanda sun kauce sun bar mutanen da ake zargin yan bindiga ne na wucewa a kan babura.
Rundunar 'yan sanda ta yi bayani
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Anietie Iniedu, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa mutanen da aka gani a bidiyon ba ‘yan bindiga ba ne.
A cewarsa, su mambobi ne na kungiyar 'yan bijilanti (VGN) da kuma mafarauta da aka yi wa rajista, wadanda ke taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyuka a yankunan Musawa da Matazu na jihar Katsina.
A sanarwar da rundunar 'yan sandan ta wallafa a shafin X, ta ce:
“Bidiyon ya nuna abin da aka saba tsakanin yan sanda da yan bijilanti, wadanda ke taimakawa harkokin tsaro yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin aiki domin tallafawa yaki da miyagu da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”
‘Yan sanda sun ce zargin karya ne
Iniedu ya jaddada cewa duk wani zargi da ke cewa jami’an ‘yan sanda suna hulda da ‘yan bindiga karya ne kuma an yi shi ne domin yaudarar jama’a.
Ya ce yaɗa irin wadannan bayanai na iya haifar da fargaba, rage amincewar jama’a da hukumomin tsaro da kuma kawo cikas ga ayyukan tsaro da ake gudanarwa.

Source: Getty Images
An gargadi masu yada labaran karya
Rundunar yan sanda ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da rahotannin da ke da alaka da bidiyon tare da rika dogaro da bayanan da hukumomin tsaro ke fitarwa a hukumance.
Ta kuma gargadi mutane ko kungiyoyin da ke kirkira ko yada labaran karya da ka iya barazana ga zaman lafiya da tsaro da cewa za a iya daukar matakin doka a kansu.
An hana yan sanda amfani da TikTok
A wani labarin, kun ji cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya haramta wa jami’an ‘yan sanda amfani da kafafen sada zumunta a Najeriya.
Dokar ta hana jami’ai dauka ko wallafa bidiyo, hotuna, barkwanci ko shirye-shirye kai tsaye cikin kayan ‘yan sanda ba tare da izini ba.
Dokar ta kuma hana jami’an yin sharhi a bainar jama’a kan binciken ‘yan sanda, ladabtarwa, sauya wurin aiki ko wasu harkokin hukuma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


