Firai minista Theresa May za ta ziyarci Najeriya a wannan makon

Firai minista Theresa May za ta ziyarci Najeriya a wannan makon

- Firai ministar Birtaniya Theresa May za ta ziyarci Najeriya

- Za ta kawo ziyarar ne a wannan mako wanda shine karo na farko da take zuwa nahiyar Afrika

- Tace tana son bunkasa da karfafa danagantakar Birtaniyar da wasu sassa na duniya

Firai ministar Birtaniya Theresa May za ta ziyarci Najeriya a wannan makon da muke ciki.

Bisa ga rubutun da aka wallafa a shafin twittar babban kwamishinan Birtaniya a Najeriya, Paul Arkwight, @paulTarkwight yace yana farin cikin tarban Firai ministar.

Misis May za ta fara ziyartar Afirka ta Kudu ne ranar Talata kafin ta isa zuwa Najeriya da Kenya a cikin shirinta na bunkasa ciniki da nahiyar bayan Birtaniya ta fice daga Tarayyar Turai.

Firai minista Theresa May za ta ziyarci Najeriya a wannan makon
Firai minista Theresa May za ta ziyarci Najeriya a wannan makon
Asali: Twitter

A cewar ta, tana son bunkasa da karfafa danagantakar Birtaniyar da wasu sassa na duniya gabanin ficewar kasar daga Tarayyar Turai.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC ta maidawa Saraki martani bayan yace bai tsoron a tsige sa

Ana kuma sa ran za ta tattauna akan batun tsaro bayan ta isa Najeriya - musamman rikicin Boko Haram da rawar da sojojin Birtaniya da aka girke a Kenya ke takawa wajen yaki da mayakan al Shabab a Somaliya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyanawa mataimakansa cewa ba ya burin sake ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari saboda "tamkar gawa" yake.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng