Buhari ya caccaki majalisar dokoki bayan an kwato N769bn na kudaden sata

Buhari ya caccaki majalisar dokoki bayan an kwato N769bn na kudaden sata

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya caccaki majalisar dokokin kasar

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya caccaki majalisar dokokin kasar ta masu laifi da aka gabatar m ata

- Yace gabatar da wannan doka ne kadai zai bayar da damar yin amfani da kudaden da aka kwato

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya Talata, 11 ga watan Satumba ya caccaki majalisar dokokin kasar akan jinkiri wajen gabatar da dokar hukunta masu laifi da aka gabatar mata.

Buhari wanda yayi magana a lokacin da kwamitin da shugaban kasa ya kafa don tantance kudaden da aka kwato suka gabatar da rahotonsu, yace makamin da zai inganta kudaden da aka kwato shine gabatar da dokar.

Ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar da su dauki matakan da suka dace wajen gabatar da dokar.

Buhari ya caccaki majalisar dokokiu bayan an kwato N769bn na kudaden sata
Buhari ya caccaki majalisar dokokiu bayan an kwato N769bn na kudaden sata
Asali: Facebook

Ya ba yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa zata ci gaba da jajircewa kan alkawarin da ta dauka na yakar cin hanci da rashawa da kuma kalubalen tsaro.

Ya bayyana cewa za’a yi nasari cikin tsanaki akan bincike da shawarwarin kwamitin domin yin aiki da su.

KU KARANTA KUMA: Ministar Buhari ta shiga matsala a gida bayan an wargaza APC

Shugaban kasar yace cin hanci da rashawa ya kasance barazana ga ci gaban kasa, tsaron kasa da kuma tattalin arzikin Najeriya.

Buhari yace ya zama dole a dauki matakan yin amfani da kamun wajen magance matsalolin tattalin arziki da na jama’a, sannan kuma ya zama dole a toshe duk wata kafa ta satar kudaden jama’a.

Kwamitin mutane uk sunce sun samo zunzurutun kudi har naira biliyan 769 a lokacin da tayi tana bincike.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel