Ana Wata ga Wata: Shugaban Kasa Ya Daga Zabe da Shekara 2

Ana Wata ga Wata: Shugaban Kasa Ya Daga Zabe da Shekara 2

  • Shugabannin mulkin soja a Guinea-Bissau sun sanar da ɗage zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa da aka shirya gudanarwa a 2026 zuwa 2028
  • Matakin ya ƙara tsawaita lokacin mulkin sojoji, duk da cewa an tsara zaɓen ne domin mayar da ƙasar ƙarƙashin mulkin farar hula
  • Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, Manjo-Janar Horta Inta-a, ne ya sanar da sabon jadawalin zaɓen a wata doka da ya fitar ranar Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Guinea-Bissau – Shugabannin mulkin soji a Guinea-Bissau sun ɗage zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a watan Disamban 2026 zuwa watan Nuwamban 2028.

Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, Manjo-Janar Horta Inta-a, ne ya sanar da sabon ranar zaɓen cikin wata doka da ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Manjo-Janar Horta Inta-a
Shugaban Guinea-Bissau, Manjo-Janar Horta Inta-a. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Aljazeera ta rahoto cewa An shirya gudanar da zaɓen ne a ranar 6 ga Disamba, 2026, domin mayar da ƙasar ƙarƙashin mulkin farar hula bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Nuwamban 2025.

Yadda sojoji suka karɓe mulki

Sojojin Guinea-Bissau sun ƙwace mulki a watan Nuwamban 2025, lamarin da ya kawo cikas ga zaɓen shugaban ƙasar tare da hambarar da tsohon shugaban ƙasa, Umaro Sissoco Embalo, wanda ke neman sake lashe zaɓe.

Bayan juyin mulkin, sojojin sun naɗa tsohon shugaban rundunar sojin ƙasar, Horta Inta-a, a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya.

An ɗaura masa alhakin jagorantar sauyin mulki na shekara guda, yayin da kundin tsarin mulkin riƙon ƙwaryar da aka wallafa a farkon watan Disamba ya hana shi tsayawa takara.

TRT ta wallafa cewa a watan Agustan 2026, 'yan ƙasar sun amince da wani sauyi a kundin tsarin mulki da ya ƙara wa shugaban ƙasa iko.

Kara karanta wannan

Bayan rashin 'yan APC 15, tsohon sakataren gwamnatin Zamfara ya rasu

Dalilin ɗage zaɓen zuwa 2028

A watan Oktoba, Firaministan ƙasar, Ilidio Vieira Te, ya bayyana cewa ba a samar da muhimman sharuɗan gudanar da zaɓe a watan Disamba ba, sai dai bai bayyana sabon lokacin da za a gudanar da zaɓen ba.

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta buƙaci a gudanar da sauyin mulki cikin gajeren lokaci, bisa tsari da kuma gaskiya, domin mayar da ƙasar ƙarƙashin mulkin farar hula.

Yadda ake rayuwa a Guinea-Bissau
Yadda jama'a ke hada-hada a Guinea-Bissau. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai sabon matakin sojojin ya nuna cewa za a ƙara tsawaita lokacin gwamnatin riƙon ƙwarya har zuwa Nuwamban 2028.

Guinea-Bissau na cikin ƙasashen da suka daɗe suna fuskantar juyin mulki da yunƙurin kifar da gwamnati tun bayan samun 'yancin kai daga Portugal sama da shekaru 50 da suka gabata.

Ana yi wa shugaban INEC barazana

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce yana samun saƙonnin barazanar kashe shi kusan kullum saboda aikinsa na jagorantar hukumar.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi rugu rugu da tawagar APC ta yi hadari, an rasa rayuka da yawa

Amupitan ya bayyana aikin INEC a matsayin wanda ba a yaba wa mai yinsa, inda ya ce jami’an hukumar na fuskantar cin zarafi da matsin lamba daga ɓangarori daban-daban.

Ya kuma gargaɗi kwamishinonin zaɓe da su guji sakaci yayin shirye-shiryen zaɓen 2027, yana mai cewa hukumar ba ta da damar yin kuskure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng