Majalisar dokoki zata bi ta kan Buhari akan kudirin gyara zabe – Dan takaran shugaban kasa a PDP

Majalisar dokoki zata bi ta kan Buhari akan kudirin gyara zabe – Dan takaran shugaban kasa a PDP

- Tanimu Turaki yayi Allah wadai da kin sanya hannu akan dokar zabe da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaki yi

- Dan takaran shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa majalisar dokokin kasar zasu sha kan shugaban kasar

- Yace abun mamaki ne cewa Shugaba Buhari yaki sanya hannu a dokar

Wani dan takaran kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Taminu Turaki, a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba, ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar zata bi ta kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan kudirin gyara dokar zabe da yayi watsi dashi.

Turaki yayinda yake Magana a Ilorin, jihar Kwara yace, abun mamaki ne cewa shugaban kasar yaki sanya a dokar. Yace shugaban kasar na tabarbara lamura ne kawai ta hanyar kin sanya hannu a dokar.

Majalisar dokoki zata bi ta kan Buhari akan kudirin gyara zabe – Dan takaran shugaban kasa a PDP
Majalisar dokoki zata bi ta kan Buhari akan kudirin gyara zabe – Dan takaran shugaban kasa a PDP
Asali: Facebook

“Abunda ke faruwa a yanzu shine ke ta faruwa a gwamnatin APC abu mai sauki day a kamata ace anyi ana mayar dashi mai wahala ba tare da wani dalili ba.

“Shugaban kasar nada iko akan sanya hannu a doka ko kin amincewa da soka. Amma a wannan lamari, gwamnatin tarayya taje kotu kuma ta fadi bayan sun fadi a yanzu kuma suna cewa sai sunyi duba.

“Allah yasa kundin tsarin mulki ta bayar da dama a wajen da za’a iya shank an lamari kuma zasuyi amfani dashi.”

Ya kara da kalubalantar gwamnatin APC da ta dunga sanya ra’ayin kasa a gaban nata a koda yaushe.

A halin da ake ciki, a kokarin gujema yiwuwar afkuwar rikici bayan zaben fidda gwaninta na yan takaran shugaban kasar ta, kwamitin amintattu na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Walid Jibrin ya bayyana cewa kwamitin na duba ga yiwuwar age yawan yan takaranta na shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe APC ta bayyana dalilin da yasa fam dinta na takara yayi tsada

Mista Jibrin ya bayyana haakan a Abuja a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba bayan wata ganawa tare da mambobin kwamitin amintattun.

Zuwa yanzu dai jam’iyyar PDP na da yan takara 13 dake neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel