2019: Matasan Kwara sun shirya wa Saraki gagarumin gangami

2019: Matasan Kwara sun shirya wa Saraki gagarumin gangami

- Kungiyar matasan Kwara sun shirya wa Saraki babban gangami

- Gangamin goyon baya ne ga kudirin shugaban majalisar dattawan na takaran kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa

- Sun yabama tsarin shugabanci irin na Saraki da kuma gudunmawarsa ga jihar Kwara

Wata kungiyar matasan jihar Kwara, a ranar Asabar, 8 ga watan Satumba yayinda take karfafa gwiwar sauran yan siyasan Najeriya da suyi koyi da tsarin shugabanci irin na shugaban majalisar dattawa sun shirya matasa domin suyi gagarumin gangami na goyon bayan kudirin takarar shugabancin Bukola Saraki.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, Abdulmajeed Olanrewaju Oba, yace akwai bukatar yin gangamin saboda gudunmawar da Saraki yaba jihar.

2019: Matasan Kwara sun shirya wa Saraki gagarumin gangami
2019: Matasan Kwara sun shirya wa Saraki gagarumin gangami
Asali: Depositphotos

Shugaban matasan wadda ya kasance jigon kungiyar Olanrewaju Oba Youth Forum (TOOYF), ya yabama Bukola-Saraki da ya amsa kiran matasan Najeiya na tsayawa takaran shugaban kasa.

Yace a halin da Najeriya ke ciki tana bukatar shugaba nagari mai kwarewa kamar Saraki domin kaita gaba akan tafarkin damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Aishat Dukku, shugaban majalisan wakilai kan harkokin zabe ta shawarci shuwagabannin addinai da su kiyayi yin suka ko hare-hare akan jam’iyyun siyasa ko yan siyasa.

Dukku, ta bada shawarar ne a wani hira tare da kamfanin dillancin labarai (NAN) a ranan Litinin, 10 ga watan Satumba, a Abuja, ta bayyana cewa shuwagabannin addinai suyi amfani da matsayinsu wajen yada zaman lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel