PDP na aiki don rage yawan yan takaran kujerar shugaban kasa – Shugaban kwamitin amintattu

PDP na aiki don rage yawan yan takaran kujerar shugaban kasa – Shugaban kwamitin amintattu

- PDP ta jero sunayen yan takaran kujerar shugaban ka a karkashinta a zaben 2019

- Saboda yawan yan takara jam'iyyar na tsoron yiwuwar barkewar rikici, don haka tana tunanin rage yan takara

- Sai dai shugabankwamitin amintattu yace jam'iyyar bazata tursasa ma kowa barin tseren ba

A kokarin gujema yiwuwar afkuwar rikici bayan zaben fidda gwaninta na yan takaran shugaban kasar ta, kwamitin amintattu na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Walid Jibrin ya bayyana cewa kwamitin na duba ga yiwuwar rage yawan yan takaranta na shugaban kasa.

Mista Jibrin ya bayyana haakan a Abuja a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba bayan wata ganawa tare da mambobin kwamitin amintattun.

Zuwa yanzu dai jam’iyyar PDP na da yan takara 13 dake neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

PDP na aiki don rage yawan yan takaran kujerar shugaban kasa – Shugaban kwamitin amintattu
PDP na aiki don rage yawan yan takaran kujerar shugaban kasa – Shugaban kwamitin amintattu
Asali: Depositphotos

Daga cikin yan takaran akwai, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal; gwamnan jihar Gombe,Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa.

Sauran yan takaran sun hada da tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mafarki, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang da kuma Datti Baba-Ahmed, sai kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark wadda ya bayyana kudirinsa a baya-bayan nan.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe APC ta bayyana dalilin da yasa fam dinta na takara yayi tsada

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan ganawar, Mista Jibrin yace yayinda suke kokarin rage yawan yan takaran kujerar shugaban kasar, jam’iyyar bazata tursasa ma kowa ya fita daga tseren ba.

Ya kara da cewa an hana mambobin kwamitin yiwa kowani dan takara kamfen.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel