Dan wasan Super Eagles zai yi wa Sakkwatawa kyauta idan suka ci Kano Pillars

Dan wasan Super Eagles zai yi wa Sakkwatawa kyauta idan suka ci Kano Pillars

Dan wasan Super Eagles, Shehu Abdullahi ya yi alkawarin bai wa kungiyar kwallon kafa ta Sokoto United kyautar kudi idan suka ci Kano Pillars.

A wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter,a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba, Abdullahi ya sha alwashin ba kulob din na Sokoto N100,000 kan kowace kwallon suka ci idan suka samu nasara a kan kungiyar Kano Pillars.

Sokoto United za ta kara da Kano Pillars a wani wasa na gasar Aieto Cup wadda ake ce wa gasar kalubale.

Dan wasan Super Eagles zai yi wa Sakkwatawa kyauta idan suka ci Kano Pillars
Dan wasan Super Eagles zai yi wa Sakkwatawa kyauta idan suka ci Kano Pillars
Asali: Getty Images

Dan wasan, wanda a yanzu haka yana taka leda a kungiyar Bursaspor ta Turkiyya, ya ce ya dauki wannan matakin ne domin nuna goyon bayansa ga tsohon kulob dinsa.

KU KARANTA KUMA: Tarihi: Birgediya Zakariya Maimalari, kwararren jami’in soja na farko a Najeriya

Duk da cewa Abdullahi ya taba buga wa Kano Pillars wasa, dan wasan ya ce ya yi sakon bidiyon ne ga hukumar gudanarwa da kuma 'yan wasan kungiyar Sokoto United.

Daga nan sai ya yi wa Sokoto United din fatan alkhairi a wasan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng