Hukumar NYSC ta gargadi yan bautar kasa da su ja baya da yan siyasa

Hukumar NYSC ta gargadi yan bautar kasa da su ja baya da yan siyasa

- Hukumar NYSC ta gargadi yan bautar kasa da zasu gudanar da zaben 2019

- Ta nemi suyi baya-baya da yan siyasa da ka so yin amfani dasu wajen cimma manufarsa

- Shugaban hukumar ya bukace su da su yi aiki da gaskiya da amana

Ganin cewa zabukan 2019 sai kara kusantowa su ke yi, wannan ya sa Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi wa Kasa Hidima, na Sashen Gudanar da Ayyukan Karkara da Ayyuka na Musamman, ya gargade su da su yi baya-baya da ‘yan siyasa.

A daidai lokacin da zabe ke sake gabatowa, shugaban hukumar kula da masu yiwa kasa hidima, ya gargade su da su ja baya da yan siyasa.

Hukumar NYSC ta gargadi yan bautar kasa da su ja baya da yan siyasa
Hukumar NYSC ta gargadi yan bautar kasa da su ja baya da yan siyasa
Asali: Facebook

Yusuf Steve ya ce masu aikin bautar kasa su yi iya bakin kokarin su don ganin sun gujema ribbatar da wasu ‘yan siyasa za su yi musu wajen ganin sun yi amfani da su wajen cimma wata boyayyar manufa a lokutan zabe.

KU KARANTA KUMA: Rayuwana da na iyalina na cikin hatsari - Atiku

Steve ya yi wannan gargadin a yau Alhamis, 13 ga watan Satumba lokacin da ya ke wa masu aikin bautar kasa na Rukunin ‘B’ na jihohin Adamawa da Taraba, jawabi a Sansanin NYSC da ke Damare, kusa da Yola.

Ya ce dukkan mambobin na NYSC da za a dauka domin gudanar da ayyukan zaben 2019, su tabbatar da cewa sun yi aiki da gaskiya, tsakani da Allah tare kuma da kishin kasa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng