Abin da IBB Ya Fada da Tawagar Tinubu Ta Ziyarci Shi da Abdussalami Abubakar

Abin da IBB Ya Fada da Tawagar Tinubu Ta Ziyarci Shi da Abdussalami Abubakar

  • Femi Gbajabiamila, ya jagoranci tawagar gwamnatin Bola Tinubu zuwa Minna domin ziyartar tsofaffin shugabannin kasa
  • Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya gaida Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar a madadin mai gidansa
  • Babangida ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu inda shi ma Abdulsalami ya yaba da ayyukansa, yana kiran a zauna lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Niger - Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya jagoranci wata babbar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Minna, jihar Neja.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da ‘yan tawagarsa sun ziyarci tsofaffin shugabannin kasa, Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Abdulsalami Abubakar.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila da Janar Ibrahim Babangida a Minna Hoto: @FemiGbaja
Source: Twitter

Femi Gbajabiamila sun ziyarci Minna a madadin shugaban kasa

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, Femi Gbajabiamila y ace Bola Tinubu ne da kansa ya umarce shi da ya kai ziyarar domin duba lafiyarsu.

Kara karanta wannan

An samu bayanin adadin gwamnonin da suke tare da Shugaba Tinubu a 2027

A yayin isar da sakon mai gidansa ga shugabannin, Gbajabiamila ya bayyana cewa Tinubu ya dade yana son zuwa domin wurin su ya ga halin da suke ciki.

Sun fara kai ziyara ga Janar Babangida mai ritaya wanda ya yi mulki tun daga 1985 zuwa 1993 gidansa da ke Hilltop, inda suka gana da shi a sirrance.

Daga bisani sun wuce gidan Janar Abdulsalami Abubakar kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

Irin rawar da kowannensu ya taka a tarihin Najeriya ya sanya su cikin muhimman mutane da ya kamata a rika tuntuba kan al'amuran kasa bini-bini.

A cewar tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar, Tinubu ya ba shi umarnin zuwa Minna ne a ranar Laraba, bayan dawowarsa daga jihar Borno.

Ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya bukace shi da ya tattauna wasu batutuwa na musamman da tsofaffin sojojin, amma bai yi karin bayani ba.

Kara karanta wannan

"Abin da ya banbanta Tinubu da Buhari, Yar'adua da sauran shugabannin Najeriya da suka gabata"

Gbajabiamila ya bayyana ziyarar a matsayin ta girmamawa, inda ya ce tun da farko sun kai ziyara ga gwamnan jihar Neja kafin su wuce gidajen su.

Babangida ya sake nuna goyon bayansa ga Tinubu

Da yake magana da ‘yan jarida bayan ziyarar, Gbajabiamila ya bayyana cewa Janar Babangida ya sake tabbatar da goyon bayansa ga Shugaba Tinubu.

Yanzu da ake tunkarar babban zabe, ya ce tsohon shugaban sojan ya nuna gamsuwarsa da gwamnatin Tinubu, tare da yi masa fatan samun nasara.

Abdulsalami ya bukaci jama'a su zauna lafiya

A nasa bangaren, shi tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana gamsuwarsa da yadda gwamnatin Tinubu ta ke tafiyar da mulki.

Yayin da ake kara kusantar zaben 2027, tsohon janar din ya yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya domin idan babu zaman lafiya, babu kasa ko zabe.

Abdulsalami ya kuma yaba wa Tinubu bisa ci gaba da kula da alakar da ke tsakaninsa da su, ya ji dadin yadda ya tuna da su duk da ana fama da yakin zabe.

Sauran mutanen da suka raka Gbajabiamila

Kara karanta wannan

Abin da Nafiu Bala ya fada wa ƴan 'takarar' ADC bayan tara su a Kaduna

Tawagar ta kunshi Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris da tsofaffin ministoci da wasu 'yan majalisar tarayya.

Rahoton ya ce sauran mutanen da suka kasance cikin tawagar sun hada da:

  • Hadiza Bala-Usman
  • Yusuf Tanko Sununu
  • Sa'idu Ahmed Alkali
  • Mataimakin gwamnan Neja, Yakubu Garba
  • Abdulmumini Jibrin Kofa
  • Fuad Kayode Laguda.
  • Dr Wasiu Olanrewaju-Smart
  • Sanusi Rikiji

Atiku Abubakar ya jefi Bola Tinubu da zargi

Ana da labari cewa yayin Bola Tinubu yake taya shi murnar cika shekaru 80, shi Atiku Abubakar yana maganar a fito da wasu kudi N1.4tr da aka batar.

Atiku Abubakar ya ce an samu gibi wajen kudin da Gwamnatin tarayya ta yi niyyar samu daga mai, ya kuma zargi gwamnati da kawo kuncin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng