Ana fada wajen tallar Tinubu, jam’iyyar APC ta fito ta yi wa Wike wankin babban bargo

Ana fada wajen tallar Tinubu, jam’iyyar APC ta fito ta yi wa Wike wankin babban bargo

  • Jam’iyyar APC reshen jihar Imo ta caccaki Ministan Abuja, Nyesom Wike, ta kira shi an aiken siyasa da ya rasa makama
  • Martanin ya biyo bayan tayin da ya yi na taimaka wa Bola Tinubu wajen samun nasara a Imo da Kwara a zaben shugaban kasa
  • APC ta ce ba ta fama da rikicin cikin gida da ke bukatar taimakon Wike, tare da zarginsa da haddasa rarrabuwar kai a Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Imo - Jam’iyyar APC ta reshen jihar Imo, ta yi wa Mista Nyesom Wike wanda shi ne Babban Ministan harkokin Abuja, wankin babban bargo.

Ganin ya fito yana neman Bola Tinubu ya kyale shi ya taimake shi a Imo, sao APC ta bayyana Nyesom Wike da gantalallen dan aike na siyasa.

Wannan martani da jam’iyyar APC ta yi domin ganin tsohon gwamnan na Rivers ya shiga taitayinsa ya zo a jaridar The Cable ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Wanda ya fara bankado zargin alakar Dan Bello da Seyi Tinubu yana cikin barazanar kisa

Wike ya bukaci shugaban kasa da kwamitin yakin zaben APC su ba shi dama ya yi masa kame a wasu karin jihohi domin ganin Bola Tinubu ya zarce.

Da yake magana a garin Gokana, jihar Rivers, ministan ya ce ya gama aikin da aka ba shi na ganin shugaba Tinubu ya yi nasara a jiharsa da kuma Abuja.

Saboda haka ne yake rokon a kyale shi ya taya jam’iyyar APC yakin zabe a jihohin Imo da Kwara.

Maganar nan sam ba ta yi wa jam’iyyar APC a Imo dadi ba, ta fitar da martani ta bakin Onwuasoanya Jones wanda shi ne sakataren yada labarai.

Onwuasoanya Jones ya fitar da jawabi jiya, inda ya ce APC ba ta fuskantar wata matsalar cikin gida da har za a kai ana neman agajin Wike a jihar Imo.

Ya kira Wike da ‘gawurtaccen ‘dan gudun hijira a siyasa’, yana mai zarginsa da kokarin Tinubu bai da farin jini sai ya nemi agaji daga wajen APC.

Kakakin na APC a Imo yake cewa burin ‘dan adawar shi ne nuna wa duniya ana bukatar taimakon wani sojan hayan PDP kafin shugaban kasa ya kai labari.

Kara karanta wannan

'Na gama da 2': Wike ya roƙi Tinubu ya kara masa jihohi 2 domin ba shi nasara a 2027

Ya ce:

""Muna so mu fito fili tun da wuri mu bayyana cewa babu wata matsala a jam’iyyar APC ta jihar Imo; yaƙin neman zaɓenmu na jam’iyya da na Shugaban Ƙasa na tafiya sumul, kuma tabbas nasara tamu ce.

A rahoton PM News, an fahimci Jones yana ganin abin da Wike yake yi na taya APC aiki alhali yana jam’iyyar adawa, ya ci karo da damukaradiyya.

Jam’iyyar APC ta reshen jihar ta ce mutanen Najeriya ba su tare da kalaman da ke kokarin nuna masu kada kuri’a ba su da amfani wajen yin nasara a zabe.

Ya ma kare da cewa Wike yana amfani da farin jinin jam’iyyar APC ne domin samun kima a siyasa har yana turo mutane da kudi su kawo matsala a jihar Imo.

Saboda haka ne ma Mista Jones ya yi kira ga Ministan na Abuja da ya yi wa jam’iyyarsa ta PDP kamfe, yana cewa yanzu fama ta ke yi har a jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng