Jijjigar kasar Abuja ba abune da ya kamata a dauka da wasa ba – Daraktan gine-gine

Jijjigar kasar Abuja ba abune da ya kamata a dauka da wasa ba – Daraktan gine-gine

Danladi Matawal darakta janar na cibiyar binciken gine-gine da titina, ya yi gargadi kan cewa kada Najeriya ta yi wa lamarin da ya faru na girizan kasa a babban birnin tarayya, Abuja rikon-sakainar-kashi.

A jawabin da ya fitar, ya bayyana cewa babu shakka akwai bukatar gwamnati ta gaggauta binciken musabbabin faruwar lamarin, wadda yaa wakana a bangarorin Abuja a ranakun Alhamis da Juma’a.

Ya ce akwai bukatar Najeriya ta fito da tsarin da zai magance sake faruwar wannan jijjigar kasa, ya-Allah ko dalilin hakar kasa ne ta faru ko kuma a’a.

Jijjigar kasar Abuja ba abune da ya kamata a dauka da wasa ba – Daraktan gine-gine
Jijjigar kasar Abuja ba abune da ya kamata a dauka da wasa ba – Daraktan gine-gine
Asali: Depositphotos

“In dai akwai inda aka rarake karkashin kasa ana gina titin karkashin kasa ko yin wani gini a karkashin kasa, to wannan gini kan iya kumbura jijiyoyin kasa har su fara jijjiga.” Inji Matawal.

“Su kan su mazauna Abuja na matukar bukatar da a horas da su matakan gaggawar da ya kamata su dauka a cikin hanzari, idan irin haka ta sake kasancewa.

“Idan wannan jijjiga kaddara ce daga Allah Ta’ala, to fa sai a yi shirin fara kwashe mutane daga Abuja ana ficewa, domin ita babbar girgizar kasa fa ta kan fara ne da ‘yar jijjigar kasa, dalili, saboda karkatsewa da daddatsewar da igiyoyi ko jijiyoyin karkashin kasa ke yi ko kuma saiwa-saiwar da ke rike da farantin da ke tallabe da jijiyoyin karkashin kasar su kan su.” Gargadin Matawal kenan.

“Wato aman wutar duwatsu da girgizar kasa duk wani balbalin bala’i ne wadanda Najeriya ba ta ma taba tunanin yi musu shirin ko-ta-kwana ba. To saboda ba a taba shirya musu din nan ba, sai jikin mu ke ba mu cewa kamar ba mu ma san da su ba, ko kuma ba mu yarda za su iya faruwa a nan ba.”

Ya ce mataki mafi sauki da kuma saurin dauka idan irin haka ta faru, to a yi gaggawar ficewa daga inda ake, a kwashi yara da kananan dabbobin da za a iya runguma, a runtuma a guje zuwa cikin fili ko sararin da babu gine-gine kusa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu yan asalin babban birnin tarayya karkashin kungiyar Coalition of FCT Indigenous Associations (CFCTIA), sun yi ikirarin cewa su ne suka haddasa girgizan kasa da ya afku a wasu yankunan babban birnin tarayyar kasa.

KU KARANTA KUMA: APC tayi Magana aka siyan fam din takara da Joshua Dariye yayi daga gidan yari

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin kungiyar, Yunusa Ahmadu Yusuf, wadda aka akewa yan jarida a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba ya gargadi mazauna Abuja da su saurari Karin irin wadannan lamari a yankunan birnin, har sai dai idan gwamnatin tarayya tayi adalci da wariyar da ake nuna masu.

Jawabin ya gargadi fadar shugaban kasa musamman Aso Villa da su tsimayi girgizan kasa, idan har ba’a nada dan asalin yankin a matsayin minister ba tsakanin yanzu zuwa Oktoba, 2018.

Ya bayyana irin wasu hukumomin gwamnati da jami’ai da suka ce girgizan kasar ya faru bisa yanayi ne a matsayin abun dariya, inda ya kara da cewa yan asalin yankin sun kasance masu zaman lafiya, amma sun tunzura saboda ba’a dauki zaman lafiyan nasu a bakin komai ba face mayar dasu saniyar ware da aka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel