Najeriya ta zargi Switzerland da masaniya kan kudaden da Abacha ya boye

Najeriya ta zargi Switzerland da masaniya kan kudaden da Abacha ya boye

Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama, ya soki lamarin kasar Switzerland cewa ta na da hannu a badakalar boye makudan kudade da tsohon shugaba na mulkin soja, Sani Abacha ya yi a kasar a lokacin ya ke kan mulki.

Onyeama ya yi zargin cewa saboda kasar na da hannu da kuma masaniya ne shi ya sa ta ke kakaba tsauraran sharudda da matakai wajen dawowa gawamnatin Najeriya da ilahirin kudaden.

Wadannan kudade dai su ne makudan kudaden da Abacha ya rika sacewa ya na kimshewa a kasashen waje, wadanda akasarin su duk miliyoyin daloli ne.

Kwanan nan ne kasar Switzerland ta amince za ta maido wa Najeriya dala 350 daga cikin makudan kudaden da Abacha ya kimshe a kasar.

Najeriya ta zargi Switzerland da masaniya kan kudaden da Abacha ya boye
Najeriya ta zargi Switzerland da masaniya kan kudaden da Abacha ya boye
Asali: Depositphotos

Ministan ya ce hankalin sa ya yi matukar tashi kuma ya fusata matuka ganin irin kudaden da Switzerland ta rike wadanda a yanzu ke a hannun wasu cibiyoyi da wasu lauyoyi a kasar.

Onyeama ya yi wannan furuci ne a ranar Talata, 11 ga watan Satumba yayin da ya ke jawabi a wurin taron shekara-shekara karo na biyu a Cibiyar Taro ta Kasa-da-kasa a Abuja.

Onyeama ya fassara matakan da kasar Switzerland ta dauka a matsayin fashi da makami ne karara da rana tsaka.

Daga nan sai ya ce kasar Switzerland na da masaniyar irin kudaden da ake sata ana kimshewa a kasar.

Sai ya ce ai dama an ce abokin barawo, shi ma barawo ne.’ Ko kuma a ce mai adana wa barawo kayan sata ai shi ma barawo ne.

Ya ce kashi 60 zuwa 65 bisa 100 na kudaden Afrika da ake sacewa, duk ana fitar da su ne ta hanyar hadin baki da manyan kamfanoni na duniya.

KU KARANTA KUMA: APC tayi Magana aka siyan fam din takara da Joshua Dariye yayi daga gidan yari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani babban Lauya na kasar waje da Gwamnatin Najeriya tayi haya domin karbo mata wasu kudin Kasar da ake zargin tsohon Shugaba Sani Abacha ya sace ya boye a Luxembourg ya zargi Ministan shari’a da kokarin yin ba daidai ba.

Enrico Monfrini ya nuna cewa Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami SAN na kokarin canza bayanin Miliyoyin kudin da Najeriya ta samu ta karbo daga kasar waje. Ministan na kokarin biyan wasu Lauyoyi bayan an karasa aikin.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Ministan shari’a na kasar watau Malami yana kokarin biyan wasu Lauyoyin Najeriya; Oladipo Okpeseyi da Temitope Adebayo Naira Biliyan 7 da sunan aiki bayan an kamalla dawowa Najeriya da kudin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel