Yanzu Yanzu: Fashewar gas yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Nasarawa

Yanzu Yanzu: Fashewar gas yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Nasarawa

Mazauna Lafia babban birnin jihar Nasarawa sun shiga tashin hankali a yau Litinin, 10 ga watan Satumba wani gidan mai kama da wuta sakamakon fashewar iskar gas.

Legit.ng ta tattaro cewa wadanda ke tashan man da suka hada da masu siyar da mai da kwastamomi duk sun kama da wuta inda da dama suka rasa ransu a gwagwarmayan.

Da dama sun kone kurmus har lahira.

Yanzu Yanzu: Fashewar gas yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Nasarawa
Yanzu Yanzu: Fashewar gas yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Nasarawa
Asali: Depositphotos

Channels TV ta rahoto cewa zuwa yanzu mutane goma ne suka mutu yayinda da dama suka ji rauni.

Rahoton ya kawo cewa daga cikin wadanda suka mutu harda karamin yaro.

An tattaro cewa wasu ababen hawa dauke da fasinjoji sun mutu a hanyar Jos.

Ga bidiyon lamarin a kasa:

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel