Kwastam sun kwace buhuhunan shinkafa 200 da aka boye karkashin sinkin ayaba

Kwastam sun kwace buhuhunan shinkafa 200 da aka boye karkashin sinkin ayaba

- Jami'an kwastam sun kama buhuhunan shinkafa yar waje guda 200

- Masu fasa kaurin sun lullube shinkafar da sinkin ayaba da yawa

- Motar da ya dauki kayan ya kai naira miliyan 2.1, yayinda haramtattun kayayyakin ya kai naira miliyan 5.1.

Jami’an hukumar kwastam na Najeriya, a jihar Imo ta kama babban mota shake da buhuhunan shinkafa 200 da aka boye da sinkin ayaba.

Shugaban kwastam na yankin Zone C, Mista Kayode Olusemire, yace an kama motar kwantanan mai dauke da lamba Lagos AGL 408 XR,a hanyar Benin na sashin a ranar Asabar, 8 ga watan Satumba.

Ya bayyana cewa kudin motar da ya dauki kayan ya kai naira miliyan 2.1, yayinda haramtattun kayayyakin ya kai naira miliyan 5.1.

Kwastam sun kwace buhuhunan shinkafa 200 da aka boye karkashin sinkin ayaba
Kwastam sun kwace buhuhunan shinkafa 200 da aka boye karkashin sinkin ayaba
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa masu fasa kaurin sun jera kayan ne sosai a cikin motar sannan suka lullube da ayaba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Sule Lamido zai janye mun a matsayin dan takara shugaban kasa a PDP - Atiku

Kwanturolan yan shawarci masu fasa kaurin da su guje ma irin wannan ayyuka, inda ya kara da cewa zasu fuskanci doka a duk lokacin da aka kama kayansu.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta hana shigo da shinkafa yar waje ne domin ta bunkasa hukumomin shinkafa yar gida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel