Sai na kwace tikitin APC daga hannun Badaru domin ya sauka daga hanyar chanji – Ubale Yusuf

Sai na kwace tikitin APC daga hannun Badaru domin ya sauka daga hanyar chanji – Ubale Yusuf

Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Jigawa, Alhaji Hashim Ubale Yusuf ya bayyana cewa zai yi takarar kujeran gwamna domin ya gyara barnar da gwamnan jihar mai ci, Muhammad Abubakar Badaru ya haddasa.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya Alhamis, 3 ga watan Satumba a jihaar Kano, Yussuf yayi zargin cewa gwamnan jihar Jigawa ya dauki wata hanya ta daban daga wacce kundin tsarin mulkin APC ke kai.

Yayi ikiarin cewa gwamnatin Badaru a Jigawa ta gaza a yankunan noma, lafiya, ilimi da kuma tsaro.

Sai na kwace tikitin APC daga hannun Badaru domin ya sauka daga hanyar chanji – Ubale Yusuf
Sai na kwace tikitin APC daga hannun Badaru domin ya sauka daga hanyar chanji – Ubale Yusuf
Asali: Depositphotos

Yayi zargin cewa gwamnatin bata aiki tare da sauran mambobin jam’iyyar APC mai mulki wajen jagorantar jihar, inda yayi korafin cewa an yasar da yan siyasa da dama da suka bayar da gudunmawawajen kafa gwamnatin.

KU KARANTA KUMA: Shugabannin kudu sun ki amincewa da sabon shugaban DSS, sun zargi Buhari da kabilanci

Da aka tambaye shi ko yayi kokarin sanya baki a cikin amarin, Yusuf yace: “Nayi kokarin sanya baki lokuta da dama amma gwamnan bai dauki shawara ta ba.

“Ya kai ta yadda har sai da na wallafa wasu shawarwari a shafin Facebook dina don wadanda ke mulki su gani su gyara, amma duk a banza.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng