Uwargidar Namadi Sambo ta nuna bacin rai kan yadda ake tozarta Musulmai masu sanya hijab

Uwargidar Namadi Sambo ta nuna bacin rai kan yadda ake tozarta Musulmai masu sanya hijab

- Uwargidar tsohon mataimakin Shugaban kasa, Amina Namadi-Sambo ta koka kan yadda akee tozarta matan Musulmi da ke sanya hiabi

- Amina ta ce hakan ya take hakkin yancin mata na yi kowace irin addini

- Ta bukaci kungiyar NASFAT da ta dauki hakkin kare musulmai mata daga irin wannan tozarcin

Uwargidar tsohon mataimakin Shugaban kasa, Amina Namadi-Sambo ta koka kan yadda akee tozarta matan Musulmi da ke sanya hiabi a wasu yankunan kasar, cewa hakan ya take hakkin yancin mata na yi kowace irin addini.

Misis Sambo ta bayyana a ranar Lahadi, 27 ga watan Janairu a Kaduna yayin kaddamar da masallacin NASFAT cewa ya zama dole a bari kowani dan Najeriya ya yi addininsa ba tare da tozarce kowani iri ba.

Uwargidar Namadi Sambo ta nuna bacin rai kan yadda ake tozarta Musulmai masu sanya hijab

Uwargidar Namadi Sambo ta nuna bacin rai kan yadda ake tozarta Musulmai masu sanya hijab
Source: UGC

“A yau matanmu na fuskantar tozarci kan sanya hijabi,” inji ta sannan ta bukaci kungiyar NASFAT da ta dauki hakkin kare musulmai mata daga irin wannan tozarcin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: N30,000 yayi kankanta a natsayi mafi karancin albashi – Dogara

Ta kuma bukaci kungiyar ta dunga ba mata tallafi ta fannin lafiya da ayyukan dogaro da kai.

A baya mun ji cewa 'Yan majalisa a kasar Birtaniya sun soma aikin tuhumar mai sa ido a wata makarantar Firamare mai suna Amanda Spielman bisa zargin nuna tsana ga 'ya'yan musulmai a makarantar da ke sa hijabi idan ta kai ziyara.

Sai dai da take maida ba'asi, ita Amanda ta musanta tuhumar inda ta ce ita kawai tana yaki ne da tilastawa yaran sa Hijabi da wasu iyayen kan yi musamman idan za su je makarantar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel