Ba mu da kudin rabawa mutane kyauta amma a kullun talaka na raina – Buhari

Ba mu da kudin rabawa mutane kyauta amma a kullun talaka na raina – Buhari

- Shugaban kasa Buhari yace gwamnatinsa ba ta da kudin kyauta da za ta dunga raba ma kowa

- Buhari yace amma za ta ci gaba da samar da kayayyakin more rayuwa a dukanin yankunan kasar da yan kudaden da ke kasa

- Dan takarar shugaban kasar a APC yace a kullun yana kwana da tashi ne da yan Najeriya a zuciyarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ba ta da kudin kyauta da za ta dunga raba ma kowa amma za ta ci gaba da samar da kayayyakin more rayuwa a dukanin yankunan kasar da yan kudaden da ke kasa.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a lokacin rufe wani taron bita da wayar da kan masu zabe wanda daraktan tsare-tsaren zabe da kula na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Abuja a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu.

Ba mu da kudin rabawa mutane kyauta amma a kullun talaka na raina – Buhari
Ba mu da kudin rabawa mutane kyauta amma a kullun talaka na raina – Buhari
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatin APC za ta ci gaba da gina karin hanyoyi, tashshin jiragen kasa, da kuma samar da wutar lantari domin habbaka asar cikin sauri.

Ya kuma kalubalanci wadanda ke gudanar da shirin da su wayar da kaan masu zabe kan bukatar su zabi APC a zabe mai zuwa.

Yace: “Dan Allah ku yi kokarin wayarwa masu zabenmu kai kan cewa sadaukarwae da suke yi a iya sanina duk daya mue domin kuri’a guda nima nake da shi.

“Ku bari su san irin matsayin da suke da shi a matsayin yan Najeriya. Don haka, muna buatar goyon bayansu da hadin kansu, ku bari su fito su zabe mu.

KU KARANTA KUMA: Magoya bayan PDP 2,509 sun sauya sheka zuwa APC a Katsina

“Ba mu d udin da za mu ba kow. Za mu yi amfani da kudin wajen samar da ababen more rayuwa – Za mu yi kokarin gina maku hanyoyinku, za mu yi kokarin gina tashoshin jiragen kasa sannan mu inganta wutar lantarki.

“Ina baku tabbacin cewa da tunanin yan Najeriya da kuma Najeriya nake kwana nake tashi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel