Kotu ta tsare mai bi ya na satar dan kamfai da kunzugun mata

Kotu ta tsare mai bi ya na satar dan kamfai da kunzugun mata

Wata kotun Majistare ta Osogbo, ta bada umarnin ci gaba da tsare wani matashi mai shekaru 23, da aka ambata da suna Peyemi Adeleke, akan zargin sa da ake yi da satar dan kamfai na mata.

Adeleke ya musanta zargin da ake yi masa na cewa an same da da abin da ba na sa ba, mallakar wata.

Mai shari’a Mary Awodele, ta ce a garkame shi a kurkuku, saboda abin da ta kira girman laifin da ya aikata.

Mai gabatar da kara Jafani Mysilimi, ya ce Adeleke ya saci dan kamfan a ranar 21 ga watan Janairu, da misalin karfe 1 na dare, a unguwar Agunwande, da ke cikin Osogbo.

Kotu ta tsare mai bi ya na satar dan kamfai da kunzugun mata
Kotu ta tsare mai bi ya na satar dan kamfai da kunzugun mata
Asali: Facebook

Ta kara da cewa dan kamfan na wata mata ce mai suna Gift Sunday.

“Jami’an ‘yan sanda sun sha wahala sosai kafin su samu nasarar karbo dan kamfan daga hannun sa. Daga nan muka kawo shi kotu.” Inji mai gabatar da kara.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta maka tsohon mijin ta a Kotu saboda tura ‘ya’yan su Almajirci a Kaduna

An dage sauraren karar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu sannan kuma alkali ta hana belin sa.

A wani lamari na daban, mun ji cewa wasu yan fashi da makami sun kai farmaki a wani bankin Polaris da ke Oke Ejigbo, Ila Orangun da ke jihar Osun.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan fashin wanda yawansu ya kai kimanin takwas sun kai hari bankin da misalin karfe 2:00 na rana , inda suka fasa kofar tsaron bankin da wani abun fashewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng