2026: Tinubu Ya Yi Martani da Dan Takarar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ekiti
- Shugaba Bola Tinubu ya taya Gwamna Biodun Oyebanji murnar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti, wanda aka gudanar a ranar Asabar
- Shugaban kasar na Najeriya ya ce nasarar Oyebanji ta nuna amincewar al’umma da ci gaba da manufofin gwamnatinsa a jihar Ekiti
- Yanzu da ya samu nasara, Tinubu ya bukaci Oyebanji da ya hada kan dukkan ‘yan jihar tare da mayar da hankali kan ayyukan raya kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu, ya taya Gwamna Biodun Abayomi Oyebanji, murnar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar, inda ya samu damar komawa mulki karo na biyu.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yabawa al’ummar Ekiti bisa yadda suka gudanar da zaben cikin lumana da tsari.

Source: Twitter
Tinubu ya yaba wa INEC kan zaben Ekiti
Bayo Onanuga ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na X jim kadan bayan hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar na Ekiti a yau Lahadi.
Shugaban kasar ya ce yadda jama’ar jihar suka sake ba Oyebanji dama ya nuna sun amince da salon mulkinsa da ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a wa’adin farko.
Tinubu ya kuma jinjinawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa kan yadda ta gudanar da zaben da hukumomin tsaro bisa kokarin tabbatar da doka da oda.
Ya bukaci INEC ta ci gaba da kokarin inganta tsarin zabe domin tabbatar da gudanar sahihan zabuka, musamman yayin da ake shirin zaben gwamnan Osun da sauran zabukan gaba.
Gwamna Oyebanji ya kafa tarihi a Ekiti
Shugaban kasar ya bayyana cewa nasarar Biodun Oyebanji ta musamman ce, kasancewar ya zama gwamna na farko a tarihin jihar Ekiti da ya samu nasarar lashe zaben komawa mulki karo na biyu a jere.
Tinubu ya ce wa’adin mulkin Oyebanji na farko ya samar da ci gaba a bangarori da dama da suka hada da ababen more rayuwa, noma, samar da ayyukan yi ga matasa, ilimi, kiwon lafiya da bunkasa yankunan karkara.
A cewarsa, sabon wa’adin da jama’a suka bai wa gwamnan kuri’a ne na amincewa da ci gaba, kwanciyar hankali da tsarin mulki mai mayar da hankali kan bukatun jama’a.

Source: Twitter
Kira ga Oyebanji bayan nasara
Shugaban kasar ya bukaci Oyebanji ya kasance mai hakuri da karamci bayan samun nasarar zabe, tare da tabbatar da cewa ya hada dukkan al’ummar Ekiti wajen tafiyar da jihar a shekaru hudu masu zuwa.
Tinubu ya kuma yabawa sauran ‘yan takarar da suka fafata da gwamnan, yana mai cewa lokaci ya yi da za a hada kai domin ci gaban jihar.
Ya ce ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki su mara wa gwamnatin Oyebanji baya wajen ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Sakon APC ga Oyebanji bayan nasara
A wani labari, mun ruwaito cewa, Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta aika da sakon taya murna ga zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026
APC ta ce Gwamna Biodun Oyebanji ya cancaci ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.
Jam'iyyar APC ta kuma jinjinawa hukumar zabe ta INEC, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki saboda kokarin da suka yi a lokacin zaben.
Asali: Legit.ng

