Manyan dalilai 3 da suka sanya ni goyon bayan shugabancin Atiku - Obasanjo

Manyan dalilai 3 da suka sanya ni goyon bayan shugabancin Atiku - Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya sake kare kansa akan shawarar da ya yanke na marawa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar baya a zabe mai zuwa.

A wani jawabi da Obasanjo ya yi yace an kira shi da sunaye iri-iri don kawai ya tsayawa tsohon mataimakin nasa.

A baya Obasanjo ya sha caccakar kudirin shugabancin Atiku inda ya bayyana shi a matsayin makaryaci sannan yace Allah ba zai taba yafe masa ba idan ya marawa kudirin shugabancin Atikun baya.

Sai dai tuni ya sanar da cewa shi ya yafe wa Atiku bayan wasu malaman addini sun shiga lamarin.

Manyan dalilai 3 da suka sanya ni goyon bayan shugabancin Atiku - Obasanjo

Manyan dalilai 3 da suka sanya ni goyon bayan shugabancin Atiku - Obasanjo
Source: Twitter

A yanzu kuma ya bayyana wasu dalilai da suka sanya shi goyon bayan dan takarar na PDP.

"Na farko shine Ka san kanka sannan ka gabatar da kanka a tadda kake. Dan Adam ajizi ne kuma yana kuskure. kada mutum ya dunga kurin cewa shi mai gaskiya da mutunci ne, yana ganin kamar shi bai taba sata ba ko shi mai amana ne duk wannan yaudara ce da cuta.

“Atiku bai taba ikirarin cewa shi tsarkakke ne ba sannan nima ban taba bayyana shi a matsayin haka ba. Ba zan taba kiran wani dan Adam a matsayin haka ba balle ma har na kira shi tsarkakakke. A lokuta da dama idan na bayyana cewa wani ba tsarkakke bane, wasu yan Najeriya kan tunzura. Gare ni, a matsayina na Kirista, tsarkakken mutum duda da nasani kuma nake dashi shine Yesu Almasihu, domin shine mai tsarki a mutane da na sani.

“Na biyu, ya zama dole ya zamo mai fada ma kansa da mutanen da yake shugabanta ko yake son shuabanta gaskiya. Dole ya zamo mai karban shawara da gyara, sannan ya zamo mai neman yafiya idan yayi kuskure ba wai ya zamo mai daura wa wasu laifukansa ba.

"Atiku yan aminta da kuskuren da yayi sannan ya nemi yafiya daga jam’yyar siyasarsa da kuma mutanen Najeriya, sannan ya nemi yafiya daga gare ni kuma na yafe masa. Koyarwar Ubangiji ne cewa mu zamo masu yafiya. Duk wanda ya ga laifi na domin yafe wa Atiku toh na barshi da Allah musamman duba ga cewa malaman addinin Kirista fa Islama sun rako Atiku wajen neman yafiya. Duk wanda baya yafiya toh bai cika mai imani ba kuma kada yayi zaton Allah zai yafe masa.

“Na uku ya zama dole shugaba ya fahimci matsalolin da yake gabansa sannan ya nemi karfin gwiwar magance su, sannan yayi kokarin neman shawarwari daga kwararru dam asana maza da mata, domin neman mafitar da zai amfani dukkanin yan Najeriya. A nawa sanin Atiku na da dukkanin wadannan cancantar a tattare da shi.”

Tsohon Shugaban kasar yace daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari har Atiku Abubakar suna da matsaloli amma dai daya yafi daya cikinsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel