Hotunan batsa ne suka yi sanadiyyar rikicin Maryam Sanda da Marigayi Bilyaminu – Shaida
Wata shaida a jiya, 22 ga watan Janairu ta bayyana cewa Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ta fada ma yan sanda cewa rikici day a kaure tsakaninta da marigayi mijinta ya faru ne sanadiyar wasu hotunan tsaraicin wata mata da ta gani a wayarsa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
An dai gurfanar da Maryam Sanda ne bisa zargin halaka mijinta, Bilyaminu Bello, wanda dan dan uwa ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Bello Halliru Muhammad. An gurfanar da ita tare da dan uwanta, Aliyu Sanda, da mahaifiyarta, Maimuna Aliyu da kuma wata Sadiya, inda kotu ke zargin Aliyu, Maimuna da Sadiya da kokarin binne laifin da Maryam ta aikata ta hanyar goge jini a wajen da abin ya faru, kamar yadda na’urar daukar hoto ta tsaro ta haska.
Bayan dawowa zaman kotu a jiya Talata, Insifekta Josephine Onyendo, wacce aka gabatar a matsayin shaida, ta bayyana wa kotu cewa, bayan an umarce ta da ta gudanar da bincike akan abinda ya faru, sai tawagarta suka nufi gidan marigayin.

Asali: UGC
“Da shigarmu gidan sai muka iske a wani labule ya karye ya fado daga masakalinsa, ga kuma dardumar sallah sannan ga ruwa a zube a kasa duk a samn benen gidan, inda a nan ne lamarin ya faru,” inji ta.
Bayan dawowar tawagar binciken daga inda abun ya faru ne sai aka umarci Maryam Sanda da ta rubuta bayanin abinda ya faru, inda ta bayyana a rubutun nata cewa:
“A ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017 wata mace ta turowa mijina hotunanta tumbur babu sutura a jikinta, wanda wannan shi ne ya haddasa fitina a tsaka ninmu”.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya aika wasika majalisar dattawa, ya zabi sabbin sunaye da za a tabbatar a matsayi jakadun kasar
Sufeta Josephine ta shaidawa kotu cewa, a yayin da ta ke kokuwa da mijin nata ne sai tukunyar shisha da ke ajiye a kasa ta fashe kuma ruwan cikin tukunyar ya zube akan tayil, dalilin da ya sanya santsi ya debi Bilyaminu ya fadi akan tukunyar kwalbar da ta fashe ya kuma samu mummunan rauni.
Maryam ta dauki mijin nata zuwa babban asibiti na Maitama, inda a nan ne aka bayyana cewa ya rasu.
Za a ci gaba da sauraron karar bisa jagorancin Mai Shari’a Yusuf Halilu a ranar 27 ga watan Fabrairu.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng