Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro

Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro

- Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro da ke Jihar Niger

- A makon da ya gabata ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin tashar jirgin ruwan

- An dai yi ginin wannan tasha mai matukar muhimmanci ga arewacin kasar akan kudi naira biliyan shida

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro da ke Jihar Niger.

A ranar Asabar 19 ga watan Janairu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin tashar jirgin.

Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro
Jirgin farko ya sauka a sabon tashar jirgin ruwa na Baro
Asali: UGC

Kakakin hukumar kula da hanyoyin jirgin ruwa na gida Mista Fadile ya bayyana cewa gwamnatin tarayya takammala ginin wannan tashar ruwa mai matukar muhimmanci musamman ga yankin Arewacin Najeriya akan kudi naira biliyan shida (N6,000,000,000).

Ya kara da cewa kamfanin kasar China, CGCC Global Project Nigeria Ltd. ce ta gudanar da aikin ginin tashar ruwan, wanda yace sun sanya na’urar janwe na daukan kaya na zama irin na tafi da gidanka.

KU KRANTA KUMA: Obasanjo na goyon bayan Atiku ne saboda tsoron abunda Buhari zai yi masa – Balarabe Musa

Baya ga na’urar daukan kaya, an kuma samar da rumfar hutawan jirgin ruwa kafin ya yi gaba, ofisoshin ma’aikata, sansanin tsaftace ruwa, na’urar bada wutar lantarki, da suran ababen bukata ta yadda tashar zata yi aiki yadda ya kamata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng