Awa 2 da ba Su Wa’adi, Masu Garkuwa Sun Sako Yan Kauyensu Sunday Igboho
- Wasu iyalai da aka sace a garin Igboho sun samu ‘yanci bayan ba su wa'adin awanni biyu kacal a jihar Oyo
- Sunday Igboho ya bai wa masu garkuwa wa’adin sa’o’i biyu su sako wadanda suka yi garkuwa da su
- Mazauna garin sun fito kan tituna suna murna tare da tarbar wadanda aka sako, ciki har da mace mai juna biyu, ‘ya’yanta da wani dan uwanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Wasu iyalai da aka ce an yi garkuwa da su a garinsu Igboho da ke Oyo sun samu ‘yanci bayan mai fafutukar kafa kasar Yarabawa.
Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya bai wa masu garkuwa wa’adin sa’o’i biyu su sako wadanda suka sace.

Source: Facebook
An sako mutanen da aka sace a Oyo
Rahotanni daga Punch suka ce sakin mutanen ya haddasa murna a fadin garin, inda mazauna yankin suka fito kan tituna domin tarbar wadanda aka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane.
An bayyana cewa cikin wadanda aka sako akwai mace mai juna biyu, ‘ya’yanta da kuma wani dan uwanta, lamarin da ya sanya jama’a farin ciki matuka.
Lamarin ya biyo bayan gargadin da Sunday Igboho ya yi wa wasu shugabannin Fulani a yankin kan karuwar hare-haren garkuwa da mutane da matsalolin tsaro.

Source: Original
Igboho ya fusata game da garkuwa da mutane
Sunday Igboho ya gana da sarakuna da wakilan al’umma inda ya nuna matukar fusata kan yawaitar garkuwa da mutane da kashe-kashe a yankin.
Ya yi zargin cewa wasu daga cikin Fulani na da hannu a ayyukan garkuwa da mutane, tare da kawo misalin wata mace mai juna biyu da kuma batun kudin fansa da aka biya.
A cewarsa, wanda ya kai kudin fansa an kashe shi yayin da aka bar mutum guda kacal da rai, yana mai cewa irin wannan abu bai kamata ya sake faruwa ba, cewar Tribune.
Sunday Igboho ya kuma bayar da wa’adin sa’o’i biyu domin a sako sauran wadanda aka yi garkuwa da su, yana mai cewa ya nuna hakuri ne saboda rokon sarakunan gargajiya.
Ya ce:
“Ni ne Sunday Igboho. Na yi shiru ne saboda iyayena sun roke ni in yi hakuri da ku. Wannan ya zama karo na karshe da irin wannan abu zai sake faruwa.”
Har ila yau, ya yi barazanar daukar mataki idan ba a sako wadanda aka sace ba, ciki har da shiga wuraren da ake zargin suna da alaka da ayyukan garkuwa da mutane.
Gwamna zai sadaukar da ransa saboda dalibai
A wani labarin, an ji cewa dalibai da malaman da 'yan bindiga suka sace a Oyo na ci gaba da zama a tsare a cikin daji wata guda bayan da aka yi garkuwa da su.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa hukumomi na ci gaba da kokarin ganin an kubutar da su cikin aminci.
Seyi Makinde ya nuna cewa a shirye yake ya sadaukar da ransa idan har hakan zai sanya yaran su kubuta daga hannun 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng

